Kimanin mutane 3 ne suka hallaka, gidaje 3000 kuma suka rushe a sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin Kwarya a kananan hukumomi 10 a jihar Yobe.
Sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA Dr. Muhammad Goje shi ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yayin da yake rabon tallafi ga wadanda bala'in ambaliyar ya shafa a kauyen Godowoli na karamar hukumar Fika a ranar Alhamis.
Sakataren hukumar ya kuma ce jihar Yobe ta hannun SEMA za ta taimaka wa duk wadanda bala'in ya shafa domin rage musu radadi.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun kunshi karamar hukumar Damaturu, da Fika, da Fune da karamar hukumar Bursari.
Sauran kananan hukumomin sun hada da karamar hukumar Machina, da Yusufari, da Gaidam, da Potiskum, da Bade da kuma karamar hukumar Nguru.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa kayayyakin da aka raba wa wadanda abin ya shafa a kauyukan Kalallawa da Godowoli sun hada da banduran kwanukan rufi da kososhi da buhunan shinkafa, da taburmi da dai sauransu.
Shugaban hukumar SEMA ya gargadi wadanda suka sami tallafin da su guji sayar da kayayyakin, kana ya bukace su da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace.














































