Wednesday, June 19, 2019

An fara nuna wa juna yatsa tsakanin Dan majalisa Hon. Lawan Sani da shugaban karamar hukumar Nguru Hon. Ali Maidami



Wannan na zuwa ne tun bayan bayyanar wani sako da Hon. Lawan Sani Inuwa dan majalisar jiha na kwaryar Nguru mai jiran gado ya rubuta a ranar Laraba a shafinsa na Facebook,  inda yake kalubalantar Hon. Ali Maidami shugaban karamar hukumar Nguru.

Duk kuwa da cewa Hon. Lawan Sani bai fito fili ya bayyana ko kan menene yake sukan shugaban ba, to amma sai dai ya kwatanta shugaban karamar hukumar da mai son tada zaune tsaye.

A sakon kazalika Hon. Lawan Sani ya kuma zargi Shugaban da yunkurin jefa matasa zaman kashe wando, tare da raba kawunan jama'a.

To sai dai a martaninsa da yammacin Larabar nan wanda Lawan Aljan Nguru ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shugaban karamar hukumar Nguru Hon. Ali Maidami ya karyata daukacin zargin dan majalisar.

Yana mai cewa zarge-zargen  ba su da tushe ballantana makama.

To sai dai a 'yan kwanakin nan an sami jita-jitar cewa akwai takaddamar da ta taso tsakanin masunta a garin da mahukuntan karamar hukumar kan batun cinikin ruwan kogi kafin masuntan su yi sun kifi a kogin Nguru.

Jita-Jitar ta ce za a siyar wa masuntan ruwan kogin ne kan farashin kudi N500,000 kuma wai an saya N200,000 amma an ce da su albarka.

Jita-Jitar ta kuma alakatanta sayar da kogin da zargin cewa wai masuntan ba su zabi jam'iyyar APC ba a zabubnukan da suka gabata.

To ko ma dai yaya ne? wannan Dandali ya yi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar kan wannan jita-jitar to amma sai dai hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba.

Wasu masu fashin bakin siyasa a Nguru sun bayyana cewa wannan wata 'yar manuniya ce dake nuna cewa Dimukradiyyar garin ta fara girma.

Hon. Lawan Sani dai dan jam'iyyar adawa ce ta PDP dake wakiltar Nguru ta tsakiya a Majalisar jiha yayin da Hon. Ali Maidami kuma dan jam'iyyar APC mai mulki ne.

No comments:

Post a Comment