Tuesday, July 16, 2019

KO A JIKINA ZARGIN RASHIN CANCANTARMU NEMAN TAKARA, KUMA SAI MUN BA WA MARADA KUNYA— Hon. Fatima Musa Walida


Daya daga cikin masu son jam'iyyar PDP  ta ba su tikitin takarar Kansila a Nguru Hon. Fatima Musa Walida, ta ce ko a jikinta zargin rashin cancanta neman takara da wata mambar jam'iyyar ta yi musu.

Hon. Walida ta kuma yi alkawarin sai ta ba wa marada kunya idan ta zama Kansila a zaben kananan hukumomi da na kansilolin jiha mai zuwa.

Tana mai tabbatar da cewa a neman takarar ta babu gudu babu ja da baya.

Walida wacce ke naman takarar Kansilar unguwar Bulabulin ta bayyana hakan ne a yammacin ranar Litinin a yayin da take mayar da martani kan zargin rashin cancantar tsaya wa takara da wata mambar jam'iyyar ta yi musu a ranar Lahadi.

Hon. Walida ta fada wa wannan Dandali cewa ita ko a jikinta don an sami wata a ra'ayinta ta ce ba su cancanci takara ba domin tana da damar ta fadi hakan.

Ta ce  Tsarin mulkin kasa ya ba ta dama kuma mutanen da suke burin tozarta wasu to shirya su ne za su tozarta.

Ta ci gaba da cewa kalaman matar ba za su sanyayar mata da gwuiwa ba, hasali ma kwarin guiwa suka ba ta domi dama a wajen Allah take nema.

Daga nan sai ta jaddada wa magoya bayanta cewa alkawaran da ta dauka idan ta zama Kansila za ta cika su  ta yadda har 'yan adawa ma za su sha mamaki.

Hon. Walida ta yi wani abu mai kama da jirwaye mai kamar wanka ga 'yan adawa,  ind ta ce ai idan ana Sallah to fa ba a magana, zai yi wuya dan Adam yayi komai daidai.

Walida wacce ke magana cikin raha da wannan Dandali ta wayar salula ta ce, ta yi amannar cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba, wanda hakan ke nuna cewa babu wani  dan Adam zai ce dari bisa dari yana aikata daidai ko da kuwa kuskuren nasa bai fito fili ba.

Ta ce tabbata ko ita ma matar da yi wannan kwatance ba ta isa ta ce tana aikata komai daidai ba, ballantana kuma har ta yi tunanin ta fi kowa.

Ta kara da cewa a baya an sha ba su labarin cewa an sami mutanen kirkin da Allah ya jarabe su da watsewa, wasunsu kuma mutanen banza ne sai Allah ya jarabce su da shiryuwa.

Ta ce mutum dai ya iya bakinsa ba dan waninsa ba ko dan kansa da iyalansa, domin rayuwar yau ba tabbas ne da ita ba.

Monday, July 15, 2019

KU KIYAYI TSAYAR DA 'YAN BARIKI TAKARA— 'Yar PDP ta fada wa Jam'iyyar a garin Nguru


Wata mata 'yar jam'iyyar PDP a Nguru ta yi kira ga shugabannin jam'iyyar da su kiyaye wajen ba wa wadanda ta kira da 'yan bariki tikitin takara domin samun nasarar jam'iyyar a zabukan shugabannin kananan hukumomi da na kansilolin jiha mai zuwa.

Matar wacce ta bukaci a boye sunanta ta fada a zantawarta da wannan Dandali ta wayar salula a ranar Lahadi cewa idan za a tsayar da 'yan takara to ya kamata a tsayar da nagartattun 'yan takara da za su iya cin zabe ba wadanda ta kwatanta da ballagazazzu ba.

Ta ce ta yi takaicin ganin wasu hotunan mata a shafukan sada zumunta ana tallatawa wadanda ta ce a ra'ayinta su ma ba su cancanci a nuna su a matsayin 'yan takara ba.

Da wakilin wannan Dandali ya tambaye ta to ko su ma matan da ta ga ana tallatawa 'yan bariki ne? Sai ta ce a a ba ta fada ba, amma dai a dukkanninsu babu wacce ta cancanci a tsayar takara.

Wakilin Dandalin ya sake tambayar ta ko wadanne mata ne suka cancanci a tsayar? Sai ta ce idan ma dole sai an tsayar da mata to a tsayar da matan aure masu daraja wadanda suka san kimar iyali da tarbiyya da za su iya kawo dukkan ci gaban da ake nema.

Matar wacce ta kira kanta mai kishin jam'iyya ta yi barazanar cewa babban kuskuren da PDP zata tafka a Nguru shi ne ta ba wa 'yan bariki takara.

Tana mai cewa ko ita a matsayinta na mambar jam'iyyar ba za ta zabi ballagazi ko ballagaza ba idan suka fito takara.

Ta ce ya kamata shugabannin jam'iyya su dubi wani abu na daban su saka wa wasu mutanen kan wahalhalun da suka sha a lokutan yakin neman zabe, amma ba jagorantar 'yan kasa ba.

To sai dai a nata bangaren, jam'iyyar PDP ta fada ta bakin Shugaban jam'iyyar na unguwar Bulabulin Rabi'u Maikaratu cewa jam'iyyar har yanzu ba ta tsayar da dan takara a mukaman da aka gano mata suke sha'awar nema ba.

Maikaratu wanda ke magana a yayin gangamin kaddamar da neman takarar Hon. Fatima Musa Walida ta Kansilan unguwar Bulabulin a ranar Asabar ya ce,  a matsayinsu na iyayen jam'iyya dole ne a kansu da su dauki kowane dan jam'iyya daidai.

Idan ba a manta ba a 'yan kwanakin nan wasu hotunan mata na ta yawo a kafafen sada zumunta wadanda ake alakanta su da neman takarar Kansila wasu Unguwanni a Nguru, al'amarin da janyo martane- martane mabambanta daga wasu mazauna garin da dama.

Saturday, July 13, 2019

An kaddamar da neman takarar Hon. Fatima Musa Walida ta Kansilan Unguwar Bulabulin a jam'iyyar PDP


Mai neman takarar Kansilan Unguwar Bulabulin a karamar hukumar Nguru a karkashin jam'iyyar PDP Hon. Fatima Musa Walida ta kaddamar da neman takararta ta neman Kansilan Unguwar.

An kaddamar da neman takarar ce a Asabar din nan a Cibiyar kallo ta Bulabulin( Bulabulin View center) cikin wani gagarumin biki da daruwan 'yan jam'iyyar suka halarta.
Wakilin wannan Dandali ya sami halartar taron ya kuma ba da labarin cewa taron ya sami hadin kan mambobin jam'iyyar.

An gabatar da jawabai daban-daban a wurin taron da galibin mahalartansa suka tashi cikin murna.
A jawabinsa na maraba, Shugaban jam'iyyar PDP na Bulabulin Rabi'u Maikaratu ya gode wa mahalarta taron tare da yin fatan a watse taro lafiya.

Rabi'u Maikaratu ya kuma ce jam'iyyar PDP na marhabin da duk wani danta da ya nuna sha'awar tsayawa takara, domin a matsayin su na iyayen jam'iyya dole ne su bi da kowa daidai.
Rabi'u Maikaratu ya ce  izuwa yanzu jam'iyyar PDP ba tsayar da dan takarar Kansila ba, to amma sai dai kowanne dan jam'iyya na hakki ya nema sannan kuma ya kaddamar da nemansa kamar yadda Walida ta kaddamar.

A nasa bangaren uban taron wanda kuma shi ne dan takarar shugancin karamar hukumar a karkashin jam'iyyar PDP Hon. Sani Garba Sharu ko Sani Gida-Gida ya yaba da yadda aka gudanar da taron.
Ita kuwa a nata jawabin da ta yi wa 'ya'yan jam'iyyar, mai neman takarar Kansilan ta Bulabulin Hon. Fatima Musa Walida gode wa Allah (SWT) ta yi tare da nuna jin dadinta game da yadda aka gudanar da taron.

Hon. Walida a jawabin ta kuma bayyana kudurorinta, wadanda ta ce idan aka zabe ta Kansila zata aiwatar wa mutanen unguwar.

Kudurorin nata dai sun hada da:

1. Kirkiro wasu hanyoyin hikima na dadada wa marayun da suke shan wahala a unguwar tare da tallafa musu da littafai da kayan makaranta domin su ma su sami rayuwa nagartacciya.

2. Za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin a ciccike ramukan da suke unguwar ta yadda za a hana ruwa kwanciya nan gaba.

3. Za ta gyara Famfunan da suka lalace wadanda aka yi watsi da su sannan kuma ta yi kokarin gina karin wasu sabbi a fadin unguwar.

4. Akwai kuma wani shiri na musanman da zata kirkiro na ciyar da unguwar gaba.
Hon. Walida daga karshe ta gode wa mahalarta taron tare da yin addu'o'in samun nasara a zaben kananan hukumomi da na kansiloli mai zuwa.

Tuesday, July 09, 2019

An kaddamar da neman takarar Hon. Sani Garba Sharu ta shugancin karamar hukumar Nguru a PDP a ranar Litinin


Daruruwan 'yan jam'iyyar PDP ne maza da mata a ranar Litinin suka taru a babban dakin taro na kamfanin Lasanco dake Nguru domin halartar babban taron kaddamar da neman takarar Hon. Sani Sharu ta shugancin karamar hukumar Nguru a karkashin jam'iyyar.

Wakilin wannan Dandali ya sami halartar babban taron ya kuma ba da labarin cewa 'yan jam'iyyar PDP sun goyi bayan mai neman takarar.

An kuma gabatar da jawabai daban-daban a wurin taron yayin da da dama daga mahalarta taron suka tashi cikin murna.

A jawabinsa ga 'yan jam'iyyar a wurin taron, mai neman takarar shugancin karamar hukumar Nguru Hon. Sani Sharu ya bayyana kudurorinsa da ya ce idan aka zabe shi zai samar wa mutanen Nguru.

Hon. Sani kamar yadda wani na hannun damarsa Habu Salisu ya jaddadawa wannan Dandali, ya yi alkawarin cewa zai samar da ci gaban da suka hada da:

1. Kirkiro wani tsari da zai taimaka wajen inganta ilimin karamar hukumar.

2. Sannan ya samar wa matasan karamar hukumar hanyoyi na musanman wajen dogaro da kai.

3. Zai yi duk mai yiwuwa wajen hada kan matasa ta hanyar wasu daburu na musanman domin ci gaban Nguru.

4. Zai inganta fannin lafiya da suka kunshi haihuwa kyauta a daukacin karamar hukumar.

5. Akwai kuma shiri na musanman na raya karkara domin jin dadin 'yan karamar hukumar.

Hon. Sani a jawabin ya kuma godewa mahalarta taron da daukacin 'yan karamar hukumar Nguru, yana mai addu'ar samun nasara a zaben kananan hukumomi mai zuwa.

Saturday, July 06, 2019

Ana ci gaba da aikin Hon. Lawan Sani na feshin maganin sauro gida-gida a garin Nguru.


Tun a ranar Larabar 3 ga watan Yulin nan ne Hon. Lawan Sani Inuwa dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya a majalisar jiha ya kaddamar da Shirin YAKI DA ZAZZABIN CIZON SAURO da aka fara da feshin magunguna a gidajen daukacin Unguwannin cikin gari guda hudu(4).

An kaddamar da Shirin ne kwanaki biyu kacal da aka gano dan majalisar da jama'arsa suna yashe wasu magudanan ruwa.

Jama'a na ci gaba da nuna jin dadi da farin ciki kan aikin feshin wanda a yau Asabar aikin ya shiga kwanaki na 5.

Wakilin Wannan Dandali ya yi kicibis da wasu ma'aikatan feshin a yau Asabar a Bulabulin ya kuma tambaye su ko yaya aikin yake gudana?

Daya daga cikin Ma'aikatan Musa Mal. Mati da aka fi sani da Kafar Yawo ya tabbatar da gamsuwar jama'a kan aikin na feshin Sauro.

Kafar Yawo wanda wakilin Dandalin ya tare shi a daidai lokacin da yake fitowa daga wani gida bayan ya feshe su da maganin a Bulabulin ta 2 ya ce aiki yana gudana kuma al'uma na ci gaba da yi wa Hon. Lawan addu'o'i.

Ya ce tunda suka somo aikin a ranar Laraba ba su fiskanci wata matsala ba, hasali ma sai tarbar arziki da suke samu gida-gida.

Kazalika Wannan Dandali ya sake kicibis da wasu ma'aikatan feshin guda biyu a a yayin da suke aikin na feshin a unguwar ta Bulabulin jim kadan bayan ya zanta da Kafar Yawo a yau Asabar.

Ma'aikatan biyu Rabi'u Muhammad da Lawan Musa su ma sun tabbatar da cewa aikin ya sami karbuwa a wurin jama'ar gari.

Suka ce mutane na tarbar su hannu biyu-biyu inda har wasu kan yi musu alherin ruwan Sanyi.


Shi ma dai shugaban ma'aikatan a unguwar Bulabulin  Sabo Pillars ya tabbatar da aikin na tafiya daidai.

Yana mai cewa tini har sun kammala da yankin Bulabulin ta 1 tun a ranar Jama'a, inda suke sa ran kammalawa da Bulabulin ta 2 da Bulabulin ta 3 daga Asabar din yau zuwa ranar Litinin din 8 ga watan Yulin 2019.
Wani sashen gari Nguru

Pillars ya ce Ma'aikatansu shida-shida aka tura sauran Unguwanni 3 da suka hada da Hausari, Tsohon Nguru da Sabon garin Kanuri a halin yanzu na ci gaba da aikin feshin safe da rana.