Monday, July 15, 2019

KU KIYAYI TSAYAR DA 'YAN BARIKI TAKARA— 'Yar PDP ta fada wa Jam'iyyar a garin Nguru


Wata mata 'yar jam'iyyar PDP a Nguru ta yi kira ga shugabannin jam'iyyar da su kiyaye wajen ba wa wadanda ta kira da 'yan bariki tikitin takara domin samun nasarar jam'iyyar a zabukan shugabannin kananan hukumomi da na kansilolin jiha mai zuwa.

Matar wacce ta bukaci a boye sunanta ta fada a zantawarta da wannan Dandali ta wayar salula a ranar Lahadi cewa idan za a tsayar da 'yan takara to ya kamata a tsayar da nagartattun 'yan takara da za su iya cin zabe ba wadanda ta kwatanta da ballagazazzu ba.

Ta ce ta yi takaicin ganin wasu hotunan mata a shafukan sada zumunta ana tallatawa wadanda ta ce a ra'ayinta su ma ba su cancanci a nuna su a matsayin 'yan takara ba.

Da wakilin wannan Dandali ya tambaye ta to ko su ma matan da ta ga ana tallatawa 'yan bariki ne? Sai ta ce a a ba ta fada ba, amma dai a dukkanninsu babu wacce ta cancanci a tsayar takara.

Wakilin Dandalin ya sake tambayar ta ko wadanne mata ne suka cancanci a tsayar? Sai ta ce idan ma dole sai an tsayar da mata to a tsayar da matan aure masu daraja wadanda suka san kimar iyali da tarbiyya da za su iya kawo dukkan ci gaban da ake nema.

Matar wacce ta kira kanta mai kishin jam'iyya ta yi barazanar cewa babban kuskuren da PDP zata tafka a Nguru shi ne ta ba wa 'yan bariki takara.

Tana mai cewa ko ita a matsayinta na mambar jam'iyyar ba za ta zabi ballagazi ko ballagaza ba idan suka fito takara.

Ta ce ya kamata shugabannin jam'iyya su dubi wani abu na daban su saka wa wasu mutanen kan wahalhalun da suka sha a lokutan yakin neman zabe, amma ba jagorantar 'yan kasa ba.

To sai dai a nata bangaren, jam'iyyar PDP ta fada ta bakin Shugaban jam'iyyar na unguwar Bulabulin Rabi'u Maikaratu cewa jam'iyyar har yanzu ba ta tsayar da dan takara a mukaman da aka gano mata suke sha'awar nema ba.

Maikaratu wanda ke magana a yayin gangamin kaddamar da neman takarar Hon. Fatima Musa Walida ta Kansilan unguwar Bulabulin a ranar Asabar ya ce,  a matsayinsu na iyayen jam'iyya dole ne a kansu da su dauki kowane dan jam'iyya daidai.

Idan ba a manta ba a 'yan kwanakin nan wasu hotunan mata na ta yawo a kafafen sada zumunta wadanda ake alakanta su da neman takarar Kansila wasu Unguwanni a Nguru, al'amarin da janyo martane- martane mabambanta daga wasu mazauna garin da dama.

No comments:

Post a Comment