Dandalin Shu'aibu Abdullahi Sa'eed Nguru,na yi wa daukacin abokan huldarsa ban gajiya,tare da murnar farawa da kuma kawo karshen babban zaben 2011 lafiya.
Dandalin na Shu'aibu,har wa yau na taya ilahirin 'yan uwa da abokanan arzikinsa,musamman masu sha'awar harkokin siyasa murnar nasarar da jam'iyyunsu suka samu a zabukan da suka gabata,kamar yadda yake taya sauran dangi takaicin rashin nasarar jam'iyyunsu a lokacin zaben,tare da fatan Allah ya ba su dangana,ya kuma sa haka shi ne mafi alheri,amin.
Hakazalika wannan Dandali,na taya dukkanin al'umar kasar nan,musamman wandada suke a yankin arewaci,alhinin abubuwan da suka faru kwanakin baya,dangane da rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa,lamarin ya janyo hasarar rayuka,da dukiyoyi masu tarin yawa,wasu kuma dubban jama'a suka rasa matsugunansu! Allah ya kiyaye faruwar haka nan gaba,ya kuma jikan musulman da suka rasa rayukansu,sa'annan ya ba wa iyalansu hakurin jure rashin. Kamar yadda Dandalin ke addu'ar Allah ya ba wa wadanda su ka sami raunuka a sakamakon rikicin lafiya.
Daga karshe,Dandalin na taya shugabannin da aka zaba murna,tare da yi musu addu'ar Allah ya ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na talakawa. Allah ya taimake mu,ya kuma albarkaci jiharmu ta Yobe,da kasarmu Najeriya baki daya,amin. Na bar ku lafiya.
Na gina wannan Dandali ne don fadakarwa da tunatarwa, tare da yin hannunka mai sanda. Wani lokaci kuma Dandalin zai zo muku da labaran gida Najeriya, da Afirka da ma duniya baki daya. Bai tsaya a nan ba, Dandalin har wa yau zai rika zuwa muku da tatsuniyoyi da almara da sauran labaran nishadi da nishadantarwa. Allah ya taimake mu.
Friday, April 29, 2011
Tuesday, April 12, 2011
"Mu za mu lashe sauran zabuka masu zuwa a Jihar Yobe"- Inji P.D.P

A karon farko tun bayan da ta sha kashi a zabubbukan 'yan majalisar tarayya da na wakilain da aka gudanar a Asabar din da ta gabata,babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Yobe,ta bayyana cewa ita ce za ta lashe sauran zabukan da suka rage.
Daraktan yakin neman zaben Sen. Usaman Albishir a 2011 na unguwar Bulabulin,a karamar hukumar Nguru,Alh. Muhammadu Kyallomi ne ya bayyana haka,jiya a wani taro da jam'iyyar ta gudanar a makarantar firamare ta Girgiri dake unguwar
ta Bulabulin.
Alh. Kyallomi,ya kuma kara da cewa,ta la'akari da yadda talakawan Yobe suke bukatar canji,da kuma yadda PDPn ta karbu a wajen jama'ar jihar,ko shakka babu PDPn ita za ta yi nasara a zubuka masu zuwa,ya kuma ce amfani da karfin mulki akan masarautun gargajiya da jam'iyyar ANPP mai mulki ta yi,wajen tursasawa jama'ar karkara zabarsu,ta hanyar yi musu barazanar karbe gonakinsu,ko shanunsu,ko gidajensu,idan suka zabi wani,ya ce shi ne musabbabin rashin nasararsu. Alh. Muhammadu Kyallomi,ya kuma gode wa matasa dangane da yadda suka fito kwai da kwarkwata suka zabi PDPn,kazalika ya bukace su da su sake fitowa a zaben ranar Asabar don zabar jam'iyyar ta PDP.
Sunday, April 03, 2011
Subscribe to:
Posts (Atom)
