Friday, October 26, 2018

PDP ta doke APC a Nguru ta tsakiya

Dan takarar majalisar jiha na jam'iyyar PDP daga Nguru ta tsakiya Hon. Lawan Sani Inuwa ya kayar da abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC Hon. Shuaibu Danladi Hamza da tazarar kuri'u 51.
A wata kuri'ar gwaji da aka kada a shafin Umar Muhammad Sanda  na Facebook wacce Adam M Adam Comrade ya raba, Hon. Lawan Sani ya sami kuri'u 81, yayin da Hon. Shuaibu Danladi kuma ya sami kuri'u 30.
Hon. Shuaibu Danladi dai shi ne dan majalisa mai ci kuma yana neman komawa majalisar ce a karo na uku.
An dai kada kuri'u 124 zuwa lokacin hada rahotan a zaben da Umar din wallafa a ran 7/10/018 da misalin 7:44 na safe. An kuma maimata kuri'u 5 a yayin kada kuri'ar, inda kuri'u 8 kuma suka kasance na 'yan ba ruwanmu.

Tuesday, August 21, 2018

Wajibin iyaye ne da su isar da amanar 'ya'yan da Allah ya ba su— Hudubar Idin babbar Sallah

An yi kira ga iyaye da su zama masu kishin iyalansu wajen kula da tarbiyyarsu domin samun tsira da samun al'uma tagari da kuma tsira a gidan duniya da na lahira.

A wani sako da kwamitin shari'a a Nguru ya aika wanda Limamin masallacin Idi na Kwalejin Atiku Abubakar da ke Nguru Al- Sheikh Umar Jinjiri da a ka fi sani da Iya da baba ya karanta yayin hudubarsa ta Sallar Idin babbar Sallah yau a garin Nguru.

Malamin ya ce wajibi ne ga iyaye da su tsare amanar da Allah ya ba su ta 'ya'ya domin samun tsira gidan duniya da lahira.

A sakon kazalika Al- sheikh Iya da baba ya bayyana cewa koke-koken da ke ta karuwa a tsanin al'umomi na bacin tarbiyya sun hada da yawaitar zinace-zinace da shaye-shaye da kuma neman maza.

Malamin ya ci gaba da cewa ba dalili ba ne al'umomi su zuba idanu ana aikata fasadi domin wai ana takamar 'yanci.

Yana mai tsawatar wa iyayen game da fadin manzon Allah na  wajibcin kawar da fasadi akan al'umomi domin gudun halaka ta gaba daya.

Friday, June 15, 2018

Kokarin nemo aibin Musulmi da yayata shi ba ya daga koyarwar Muslumci — Hudubar Juma'a

An yi kira ga al'umar Musulmai da su zama masu rufe asirin 'yan uwansu domin ribatar rayuwar duniya da ta lahira.  

Babban limamin masallacin Juma'a na Kwalejin Atiku Abubakar da ke Nguru Al-sheikh Umar Jinjiri wanda aka fi sani da Iya da Baba, shi ne ya yi wannan kiran a hudubarsa ta Sallar Juma'a yau a garin Nguru.

Sheikh Iya da Baba ya ce akwai bukatar Musulmai da su rungumi al'adar nan ta sakaye sirrin junansu musamman ma ga abubuwan da ka iya ragewa juna kima.

Malamin a hudubar tasa ya kuma gargadi Musulman da su nisantar da kansu kacokan wajen binciko sirrin dan uwansu da Allah ya rufe tare da kokarin yayata shi.

Yana mai cewa yin hakan ita ce karantarwar addinin ga Musulmai.

Malamin daga karshe ya rufe da Hadisin Manzon Allah ( SAW), inda ya bukaci manya daga cikin Musulmai su tausawa kananansu, yayin da kananan su kuma su girmama wadanda suka fisu yawan shekaru.