Sunday, July 26, 2020

Kwamitin shari'a a Nguru zai tattauna kan sha'anin aure a ranar Lahadi


Kwamitin shari'ar addinin Muslunci a Nguru (Nguru Shari'a Implementation Committee) zai tattauna kan al'amuran auratayya wacce ake gani ta tabarbare a tsakanin al'uma.

Wani mamban kwamitin Malam Muhammad Sani Alhasan ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Asabar cewa, ganarwar za a gudanar da ita ne a yau Lahadi a masallacin Juma'a na kofar fada da misalin karfe 10 na safe, inda za a tattauna batun manyan matsaloli 2 da suka yi wa aure dabaibayi tare da lalubo hanyoyin magance su.

Malam Alhasan ya ce 'yan kwamitin za su tattauna batun matsalolin aure da kuma tsirface-tsirfacen da a cewarsa su suke janyo tsadar aure.

Wasu da dama dai na ra'ayin cewa rashin fahimtar hakikanin aure kafin yin sa, da kwadayi da babban buri, tare kirkirarrun al'adun aure na taka muhimmiyar rawa wajen karuwar mace-macen aure da raguwar yinsa a tsakanin matasa.

Monday, July 20, 2020

Tsohuwa mai shekara 107 ta warke daga corona a kasa mai tsarki


Wata tsohuwa 'yar shekara 107 a kasa mai tsarki ta warke a asibitin Jeddah bayan ta kamu da cutar Corona.

Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa babban darakta a asibitin Jeddah, Dokta Khaled Al-Ghamdi ya ce tsohuwar ta yi ta fama da matsalar numfashi, inda a ka garzaya da ita zuwa sashen samun kulawar gaggawa inda tawagar manyan likitoci karkashin jagorancin Dokta Ruba Hindi suka sa ido har warkewarta.

BBC ta ce tsohuwar ta nuna alamomin cutar da suka kai ga ta kamu da pneumonia da karancin numfashi, hakan ya tilasta aka sa mata na'urar da ke taimaka wa numfashi har na tsawon kwana hudu.

Yanzu haka an sallame ta bayan an tabbatar da cewa ta samu cikakkiyar lafiya.

Hukumomin asibitin sun ce yanzu haka ta murmure kuma babu wani ciwo da ke tattare da ita.