Tuesday, August 23, 2011

Binciken ba sani ba sabo ya yi awon gaba da aiyukan daruruwan ma'aikata a garin Nguru.


Kimanin ma'aikatan karamar hukuma sama da 1300 da ake zargin an dauka aiki ba bisa ka'ida ba ne suka rasa aikinsu a karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe.

Ma'aikatan sun yi bankwana da aikin nasu ne sakamakon wan bicike da gwamnatin jihar ta gudanar a karshen watan jiya na Yuli, a cewarta da nufin kakkabe bara-gurbin ma'aikata.

Binciken da aka gudanar a karamar hukumar ta Ngurun kamar yadda wata majiya ta shaidar, ya biyo bayan zarge-zargen juna ne da aka fara,  a tsakanin tsohon shugaban karamar hukumar Alh. Muhd Wali Shettima da ya sauka kwanannan, da tsohon shugaban ma'aikatan karamar hukumar Alh. Tijjani Bakabe, inda kowannensu ke zargin juna da daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba, lamarin da ya ja hankalin gwamnati a jihar a kan ta gudanar da bincike.

Sai dai wannan Dandali ya samu a wata majiya cewa, nan ba da dadewa ba ne ake sa ran kwamitin da ya gudanar da binkicen,karkashin wanda Chiromari ka jagoranta, zai sake tantance wasu daga cikin korarrun ma'aikatan domin dawo da su bakin aikinsu.

Dama dai tun da farko, gwamnatin ta jihar Yobe ta kuduri aniyar rage ma'aikatanta,wanda ta ce ta hakan ne za ta samun damar iya biyan mafi karancin albashin ma'aikata na N18,000.00 da gwamnatin tarayya ta amince da shi, al'amarin da wasu ke ganin cewa sallamar ma'aikatan ce gwamnatin ta somo.

Friday, August 05, 2011

An bukaci Musulmai da su dinga taimakon juna cikin Ramadana.




An bukaci al'umar Musulmai da su zama masu taimakon junansu,musamman a kwanakin watan Azumin Ramadan don cin ribar rayuwa.

Babban limamin masallacin Juma'a na kungiyar Jama'atu Izalatul bid'a wa iqamatus sunna Al-shaikh Muhammad Khamis Ya'u Bello ne ya bukaci hakan a hudubarsa ta Sallar Juma'a yau a garin Nguru.

Shaikh Khamisu ya kara da cewa, watan Ramadana wata ne da ake bukatar duk wani Musulmi ya rubanya ibadunsa ga Allah (S.W.T), tare da yawaita karatun Alkur'ani mai girma da kauracewa ayyukan assha.

Shehun malamin har wa yau ya bukaci musulmin da su zama masu yawaita kyaututtuka, da sadaka ta hanyar taimakawa gajiyayyun cikinsu da abinci ko sutura, da kuma sauran kayayyaki irin na masarufi. A cewarsa ta haka ne 'yan uwantakar addini zata kara karfi.

Hakazalika malam Khamisu ya kawo ayoyi daga cikin Al,kur'ani mai girma, da Hadisan manzon Allah (S.A.W), inda ya tunatar wa musulman game da falalar ciyar da mai yin azumi da kyautata masa, ya ce yin hakan shi ne cin ribar rayuwa.

Al-shaikh Khamisu daga karshe, ya yi addu'ar fatan alheri, tare da addu'ar samun zaman lafiya ga mazauna garin Maidugiri ta jihar Borno da ma Najeriya baki daya.

Wednesday, July 20, 2011

An bukaci matasa masu yi wa kasa hidima da su dogara da kansu a rayuwa.


An bukaci matasa 'yan yi wa kasa hidima da su zama masu dogaro da kansu a duk inda suka sami kansu a rayuwa.

Shugaban hukuma mai kula da 'yan yi wa kasa hidima ta kasa,Birgediya Mahrazu Isma'ila Tsiga ne ya bukaci hakan jiya a lokacin da ya ziyarci sansanin horar da matasa 'yan yi wa kasa hidima dake karamar hukumar Girie ta jihar Adamawa.

Birgediya Tsiga,wanda shugabar hukumar mai kula da jihohin Arewa maso gabar madam Roda Kaka Kwaki ta wakilta,ya ce matasan 'yan yi wa kasa hidima wani madubi ne na al'uma,wadanda sai da su ne kasa zata ci gaba.

Madam Kwaki har wa yau ta bayyana matasan da cewa su ne kashin bayan ci gaban kowace al'uma ta da da ta yanzu. A cewarta ya zama dole ga matasan da su zama masu dogaro da kai ta hanyar yi tare da kirkirar sana'o'i,kazalika madam Kwaki ta ce hukumarsu a shirye take da ta taimaka wa irin wadannan matasa don ganin sun sami hanyar dogaro da kansu bayan sun kammala ayyukansu na hidimar kasa.

Daga karshe,madan Kwaki ta tabbatar wa matasan karin albashinsu da gwamnatin tarayya ta yi musu na N19800,maimakon N9700n da aka saba biya a baya. Sa'annan ta bukace su da zama masu hali nagari a duk inda suka sami kansu a fadin jihar ta Adamawa.

Friday, June 03, 2011

Majalisar Yobe ta dakatar da sabon babban Khadi na jihar.


A zamanta na jiya Alhamis, majalisar dokoki ta jihar Yobe, ta dakatar da sabon babban Khadi na jihar Khadi Ibrahim Ahmad daga mukaminsa.

Dakatarwar ta biyo bayan wata takardar korafi da Khadi Shu'aibu Talba ce ya gabatar wa kwamiti mai sa ido akan harkar shari'a na majalisar, inda a cikinta yake kalubalantar cancantar Ahmad.

Khadi Talba har wa yau a korafin nasa ya bayyana wa majalisar cewa kuskure a nada Khadi Ahmad matyayin Babban Khadi, yana mai cewa tun da dai ya girme shi ta fuskar aiki. 


Ya kuma kwatant hakan da cewa wata makarkashiya ce ake kokarin kullawa.


Ra'ayoyi dai sun banbanta a zauren majalisar, inda wasu mambobi ke ganin Khadi Ibrahim Ahmad ne ya cancanci mukamin na babban Khadi na jihar ta Yobe, yayin da wasu mambobin ke ganin cancantar hakan akan Khadi Talba.


Tuni dai majalisar ta dakatar da Khadi Ahmad har sai an gudanar da bincike, inda a nan take kakakin majalisar Hon. Usman Adamu ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike akan lamarin.


An kuma bukaci kwamitin da ya gabatar da rahoton binciken nasa a ranar 14 ga wannan wata na Yuni lokacin da 'yan majalisar zasu dawo zama. -Dailytrust newspaper of 3 june 2011

Friday, April 29, 2011

Sakon Dandalin Shu'aibu na bayan Zaben 2011.

Dandalin Shu'aibu Abdullahi Sa'eed Nguru,na yi wa daukacin abokan huldarsa ban gajiya,tare da murnar farawa da kuma kawo karshen babban zaben 2011 lafiya.

Dandalin na Shu'aibu,har wa yau na taya ilahirin 'yan uwa da abokanan arzikinsa,musamman masu sha'awar harkokin siyasa murnar nasarar da jam'iyyunsu suka samu a zabukan da suka gabata,kamar yadda yake taya sauran dangi takaicin rashin nasarar jam'iyyunsu a lokacin zaben,tare da fatan Allah ya ba su dangana,ya kuma sa haka shi ne mafi alheri,amin.

Hakazalika wannan Dandali,na taya dukkanin al'umar kasar nan,musamman wandada suke a yankin arewaci,alhinin abubuwan da suka faru kwanakin baya,dangane da rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa,lamarin ya janyo hasarar rayuka,da dukiyoyi masu tarin yawa,wasu kuma dubban jama'a suka rasa matsugunansu! Allah ya kiyaye faruwar haka nan gaba,ya kuma jikan musulman da suka rasa rayukansu,sa'annan ya ba wa iyalansu hakurin jure rashin. Kamar yadda Dandalin ke addu'ar Allah ya ba wa wadanda su ka sami raunuka a sakamakon rikicin lafiya.

Daga karshe,Dandalin na taya shugabannin da aka zaba murna,tare da yi musu addu'ar Allah ya ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na talakawa. Allah ya taimake mu,ya kuma albarkaci jiharmu ta Yobe,da kasarmu Najeriya baki daya,amin. Na bar ku lafiya.

Tuesday, April 12, 2011

"Mu za mu lashe sauran zabuka masu zuwa a Jihar Yobe"- Inji P.D.P


A karon farko tun bayan da ta sha kashi a zabubbukan 'yan majalisar tarayya da na wakilain da aka gudanar a Asabar din da ta gabata,babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Yobe,ta bayyana cewa ita ce za ta lashe sauran zabukan da suka rage.
Daraktan yakin neman zaben Sen. Usaman Albishir a 2011 na unguwar Bulabulin,a karamar hukumar Nguru,Alh. Muhammadu Kyallomi ne ya bayyana haka,jiya a wani taro da jam'iyyar ta gudanar a makarantar firamare ta Girgiri dake unguwar
ta Bulabulin.
Alh. Kyallomi,ya kuma kara da cewa,ta la'akari da yadda talakawan Yobe suke bukatar canji,da kuma yadda PDPn ta karbu a wajen jama'ar jihar,ko shakka babu PDPn ita za ta yi nasara a zubuka masu zuwa,ya kuma ce amfani da karfin mulki akan masarautun gargajiya da jam'iyyar ANPP mai mulki ta yi,wajen tursasawa jama'ar karkara zabarsu,ta hanyar yi musu barazanar karbe gonakinsu,ko shanunsu,ko gidajensu,idan suka zabi wani,ya ce shi ne musabbabin rashin nasararsu. Alh. Muhammadu Kyallomi,ya kuma gode wa matasa dangane da yadda suka fito kwai da kwarkwata suka zabi PDPn,kazalika ya bukace su da su sake fitowa a zaben ranar Asabar don zabar jam'iyyar ta PDP.

Sunday, April 03, 2011

Labari da dumi-duminsa: Hukumar zabe ta sake dage zabe zuwa ranar Asabar.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta sake dage zaben 'yan majalisar tarayya da za a gudanar da a gobe litinin zuwa ranar Asabar ta mako mai zuwa.

Saturday, March 19, 2011

Za a yi amfani da jiragen sama masu saukar Angulu wajen gudanar da zabe a jihar Yobe.


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Yobe, ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryenta na samar da jiragen sama masu saukar Angulu don gudanar da ayyukan zabe a jihar Yobe.

Baturen zaben jihar Malam Sadiq Musa shi ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a Damaturu.

Malam Musa ya ce za a yi amfani da jiragen ne domin saukaka ayyukan zabe a kananan hukumomi 12 daga cikin kananan hukumomi 17 na jihar wadanda hukumar tasa kan fuskanci matsaloli daban-daban sakamakon yawaitar hamadar sahara a lokutan zabe.

Ya kara da cewa ana sa ran isowar wadannan jirage nan da karshen wannan wata.

Daga nan sai ya bukaci jam'iyyun siyasa da masarautun gargajiya, tare da shugabannin addinai, da kungiyoyi daban-daban, da su ba wa ma'aikatan hukumarsa hadin kai a lokutan babban zabe mai zuwa,don ganin an gudanar da zabe mai tsafta a dukkan fadin jihar.

Monday, March 07, 2011

P.D.P ba zata iya cin zabe ba a jihar Yobe. Inji ANPP.


Jam'iyyar ANPP mai jan ragamar mulkin jihar Yobe,ta ce daga dukkanin alamu,ANPP ita zata sake danewa karagar mulkin jihar,a babban zabe mai zuwa.
Shugaban jam'iyyar ANPP na jihar,Alh. Sani Inuwa Nguru ne ya bayyana haka,lokacin zantawarsa jiya da wakilin jaridar Leadership,a gidansa dake garin Damaturu.
Inuwa wanda kuma ya kara da cewa "idan aka lura da yanayin siyasar yanzu,to fa babu shakka suke da Nasara".
Kazalika ya yi nuni akan irin tazarar da jam'iyyar tasa ta yi wa P.D.P a jihar. A cewarsa "muke da gwamna,da mataimakin gwamna,tare da 'yan majalisar jihar 19 daga 24,kuma kowannensu ba ya shakkar mutanensa".
Ya kuma ce "ai tun farkon kafuwar Dimukradiyyar nan, a shekarar 1999,P.D.P ba ta taba yin Nasara ba,ba kuma ta yi Nasarar ba,mu kadai za mu yi ta mulki a jihar har abada.- Leadership Newspaper.