Friday, August 23, 2019

MUTANE 3 SUN MUTU, GIDAJE 3000 SUN RUSHE A AMBALIYAR RUWA A JIHAR YOBE


Kimanin mutane 3 ne suka hallaka, gidaje 3000 kuma suka rushe a sakamakon ambaliyar ruwa da ta faru a sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin Kwarya a kananan hukumomi 10 a jihar Yobe.

Sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA Dr. Muhammad Goje shi ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yayin da yake rabon tallafi ga wadanda bala'in ambaliyar ya shafa a kauyen Godowoli na karamar hukumar Fika a ranar Alhamis.

Sakataren hukumar ya kuma ce jihar Yobe ta hannun SEMA za ta taimaka wa duk wadanda bala'in ya shafa domin rage musu radadi.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun kunshi karamar hukumar Damaturu, da Fika, da Fune da karamar hukumar Bursari.

Sauran kananan hukumomin sun hada da karamar hukumar Machina, da Yusufari, da Gaidam, da Potiskum, da Bade da kuma karamar hukumar Nguru.

Jaridar Daily Post ta rawaito cewa kayayyakin da aka  raba wa wadanda abin ya shafa a kauyukan Kalallawa da Godowoli  sun hada da banduran kwanukan rufi da kososhi da buhunan shinkafa, da taburmi da dai sauransu.

Shugaban hukumar SEMA ya gargadi wadanda suka sami tallafin da su guji sayar da kayayyakin, kana ya bukace su da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace.

Thursday, August 22, 2019

KOTUN SAURAREN KARARRAKIN ZABE A JIHAR KANO TA YI BARAZANAR MAYAR DA ZAMANTA ZUWA ABUJA


Kotun sauraren kararrakin zabe dake zamanta a jihar Kano ta yi barazanar sauya matsugunninta zuwa Abuja muddun aka yi wa wani mambanta barazana a jihar.

Alkaliyar Kotun mai shari'a Halima Shamaki Muhammad ita ce ta fadi hakan a yayin da take Allah wadai da wani farmaki ta internet da aka kai wa daya daga cikin shaidun hukumar zabe wacce ta bayar da shaida a gaban kotun

Mai shari'a Halima ta ce tana daya daga cikin wadanda suka nace akan cewa Kotun sai ta gudanar da zamanta a jihar Kano domin ta ba wa mutanen jihar damar gani da jin abubuwan dake wakana a kotun.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa matakin na kotun ya biyo bayan korafin Lauyan hukumar Zabe Adedayo Adedeji wanda ya sanar da kotun cewa an kai wa daya daga cikin shaidun hukumar Halima Sambo Hasan farmaki ta kafafen sada zumunta.

Halima Sambo Hasan dai ita ce Jami'ar hukumar ta karamar hukumar Ungoggo an dauki hotonta a bayan ta ba da shaida an kuma watsa hotunan a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya inda ake alakanta ta da gwamnatin jihar lamarin da ya sa mutane suka farmake da kalaman zagi.

Adedeji ya kuma kwatanta lamarin a matsayin wulakanta kotu, inda ya roki kotun da ta dauki matakin da ya dace.

Shi ma dai Lauyan jam'iyyar PDP Maliki Kuliya Umar ya yi Allah wadai da abin da ya faru inda ya kwatanta shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, kana ya kira shi da cin mutuncin shari'a.

A hukuncinta mai shari'a Halima ta ba da umarnin hukumomin da suka dace da su  gudanar da bincike akan lamarin.

Friday, August 16, 2019

An kwatanta Wakilcin Hon. Lawan Sani da na Sayyadina Umar (R.A)


Jama'a a garin Nguru jihar Yobe har ma da wasu a wajen Nguru na ci gaba da shi albarka ga dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya a majalisar jiha Hon. Lawan Sani.

Wannan fatan alheri na zuwa ne tun bayan bayyanar wani hoto da  Hon. Lawan Sani ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis a cikin ruwan sama.

A hoton an gano dan majalisar a gidajen wasu talakawa da ruwa ya mamaye a sakamakon ruwan sama kamar da bakin   Kwarya da aka shafe awoyi ana tafka shi tun da asubahin ranar Alhamis a garin Nguru.

Dan majalisar da aka kwatanta aikinsa da na Sayyadina Umar(R.A) ya rubuta cewa mutanen da bala'in ya shafa za su sami tallafi daga kungiyoyin agajin gaggawa tare da gwamnatin jihar Yobe.

Hon. Lawan ya ce: "A yau da karfe shida na safe 6:00am na fita dan naga irin damuwar da al'ummar mu suka shiga ah sa nadiyar ruwan sama kuma Inshaa Allah Gomnatin Yobe zata kawo mana gudun mawa"( and other agencies for intervention). Allah Ya taimaki Al'ummar mu!!!".

Tun daga bayyanar sakon ne jama'a ta ci gaba da martani inda wasu suka ce abin da dan majalisar ya yi aiki ne irin na magabatan farko.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa dan majalisar dake wakiltar Nguru a karo na farko bayan ya kada na jam'iyyar APC mai ya shiga an kwashe ruwan da ya mamaye wadannan gidaje ba tare da ya sanar da kowa ba.

Ruwan saman na ranar Alhamis ya janyo asara mai yawa da rushewar gidaje al'amarin da ya raba mutane da dama da mahallansu.

Kazalika wasu rahotanni a yau Juma'a sun tabbatar da cewa Hukumar agajin gaggawa ta SEMA ta iso garin Nguru domin kididdige adadin wadanda bala'in ambaliyar ruwan ya shafa.

Ishaq Rabi'u Ishaq daya ne daga cikin mazauna Nguru ya ce abin da dan majalisar ya aikata aiki ne irin na Sayyadina Umar a lokacin yana Khalifan Muslumci.

Idan ba a manta ba, ko a 'yan satikan da sukan da suka wuce an gano dan majalisar a cikin magudanan ruwa yana yashe su tare da jama'arsa, kafin daga bisani a gano shi a makabarta yana feshin ciyawa tare da gyara wasu kaburburan da suka rufta.

Sunday, August 11, 2019

An kammala yanka da rabon naman Saniyar Mr. Las ta Unguwar Bulabulin.


A kokarinsa na ganin ya samar wa matasa da al'umomin unguwannin cikin gari guda hudu da dan abin kai wa bakin salati na naman Sallah, Hon. Lawan Sani dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya ya yanka katuwar Saniyar da ya gabatar wa al'umar unguwar Bulabulin.

Saniyar wacce Alaramma Gwani Sulaiman ya yanka a yau Lahadi an yanka ta ne da misalin karfe 10: 52 na safe bayan an sauko daga Sallar Idi.

An yanka Saniyar ce a gaban gwamman jama'a da taimakon wakilan yankan
karkashin kulawar Malam Rabi'u Maikaratu.

Wakilin wannan Dandali ya sami halarta wurin yankan ya kuma ba da labarin cewa an rararraba naman Saniyar ga mabukata, inda galibin wadanda suka halarci wurin yankan sun sami naman.
Duk kuwa da cewa harkar jama' ba zai yiwu a kasa samun wasu 'yan korafe-korafe ba, to amma sai dai inji wakilinmu  za a iya cewa aikin ya sami nasara.

Wasu da suka samu naman sun nuna jin dadinsu game da wannan gagarumar Layya da Hon. din ya yi musu.

Suna masu cewa sun gamsu da wakilcin dan majalisa Lawan Sani.

Taron yankan wanda aka bayyana a matsayin na farko a tarihi ya sami halarta gwamnan magoya baya daga sassa daban-daban na unguwar da suka hada da Malam Rabi'u Maikaratu, da Sabo Pillars, da Malam Umar Haruna Famasi na hukumar kula da jidagen Yari ta kasa( Nigeria Prison Service),da wani wanda ake kira Teteyi.

Akwai kuma Danjuma mai aski, da Sagiru kira, da Allai Madu Guba tare kuma da Hon. Abubakar Man B.K mai neman takarar Kansilan Unguwar Bulabulin.

Sauran mahalarta wurin yankan sun hada da Alhaji Garba da Abdullahi Dan mai kosai da aka fi sani da Kawu Lele, da Bala An gaishe shi da Erg. Mado da Dan Asabe Fanis, da Isibu Journalist da dai sauransu.