Kotun sauraren kararrakin zabe dake zamanta a jihar Kano ta yi barazanar sauya matsugunninta zuwa Abuja muddun aka yi wa wani mambanta barazana a jihar.
Alkaliyar Kotun mai shari'a Halima Shamaki Muhammad ita ce ta fadi hakan a yayin da take Allah wadai da wani farmaki ta internet da aka kai wa daya daga cikin shaidun hukumar zabe wacce ta bayar da shaida a gaban kotun
Mai shari'a Halima ta ce tana daya daga cikin wadanda suka nace akan cewa Kotun sai ta gudanar da zamanta a jihar Kano domin ta ba wa mutanen jihar damar gani da jin abubuwan dake wakana a kotun.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa matakin na kotun ya biyo bayan korafin Lauyan hukumar Zabe Adedayo Adedeji wanda ya sanar da kotun cewa an kai wa daya daga cikin shaidun hukumar Halima Sambo Hasan farmaki ta kafafen sada zumunta.
Halima Sambo Hasan dai ita ce Jami'ar hukumar ta karamar hukumar Ungoggo an dauki hotonta a bayan ta ba da shaida an kuma watsa hotunan a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya inda ake alakanta ta da gwamnatin jihar lamarin da ya sa mutane suka farmake da kalaman zagi.
Adedeji ya kuma kwatanta lamarin a matsayin wulakanta kotu, inda ya roki kotun da ta dauki matakin da ya dace.
Shi ma dai Lauyan jam'iyyar PDP Maliki Kuliya Umar ya yi Allah wadai da abin da ya faru inda ya kwatanta shi a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, kana ya kira shi da cin mutuncin shari'a.
A hukuncinta mai shari'a Halima ta ba da umarnin hukumomin da suka dace da su gudanar da bincike akan lamarin.

No comments:
Post a Comment