Saturday, March 19, 2011

Za a yi amfani da jiragen sama masu saukar Angulu wajen gudanar da zabe a jihar Yobe.


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Yobe, ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryenta na samar da jiragen sama masu saukar Angulu don gudanar da ayyukan zabe a jihar Yobe.

Baturen zaben jihar Malam Sadiq Musa shi ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a Damaturu.

Malam Musa ya ce za a yi amfani da jiragen ne domin saukaka ayyukan zabe a kananan hukumomi 12 daga cikin kananan hukumomi 17 na jihar wadanda hukumar tasa kan fuskanci matsaloli daban-daban sakamakon yawaitar hamadar sahara a lokutan zabe.

Ya kara da cewa ana sa ran isowar wadannan jirage nan da karshen wannan wata.

Daga nan sai ya bukaci jam'iyyun siyasa da masarautun gargajiya, tare da shugabannin addinai, da kungiyoyi daban-daban, da su ba wa ma'aikatan hukumarsa hadin kai a lokutan babban zabe mai zuwa,don ganin an gudanar da zabe mai tsafta a dukkan fadin jihar.

Monday, March 07, 2011

P.D.P ba zata iya cin zabe ba a jihar Yobe. Inji ANPP.


Jam'iyyar ANPP mai jan ragamar mulkin jihar Yobe,ta ce daga dukkanin alamu,ANPP ita zata sake danewa karagar mulkin jihar,a babban zabe mai zuwa.
Shugaban jam'iyyar ANPP na jihar,Alh. Sani Inuwa Nguru ne ya bayyana haka,lokacin zantawarsa jiya da wakilin jaridar Leadership,a gidansa dake garin Damaturu.
Inuwa wanda kuma ya kara da cewa "idan aka lura da yanayin siyasar yanzu,to fa babu shakka suke da Nasara".
Kazalika ya yi nuni akan irin tazarar da jam'iyyar tasa ta yi wa P.D.P a jihar. A cewarsa "muke da gwamna,da mataimakin gwamna,tare da 'yan majalisar jihar 19 daga 24,kuma kowannensu ba ya shakkar mutanensa".
Ya kuma ce "ai tun farkon kafuwar Dimukradiyyar nan, a shekarar 1999,P.D.P ba ta taba yin Nasara ba,ba kuma ta yi Nasarar ba,mu kadai za mu yi ta mulki a jihar har abada.- Leadership Newspaper.