Kimanin ma'aikatan karamar hukuma sama da 1300 da ake zargin an dauka aiki ba bisa ka'ida ba ne suka rasa aikinsu a karamar hukumar Nguru ta jihar Yobe.
Ma'aikatan sun yi bankwana da aikin nasu ne sakamakon wan bicike da gwamnatin jihar ta gudanar a karshen watan jiya na Yuli, a cewarta da nufin kakkabe bara-gurbin ma'aikata.
Binciken da aka gudanar a karamar hukumar ta Ngurun kamar yadda wata majiya ta shaidar, ya biyo bayan zarge-zargen juna ne da aka fara, a tsakanin tsohon shugaban karamar hukumar Alh. Muhd Wali Shettima da ya sauka kwanannan, da tsohon shugaban ma'aikatan karamar hukumar Alh. Tijjani Bakabe, inda kowannensu ke zargin juna da daukan ma'aikata ba bisa ka'ida ba, lamarin da ya ja hankalin gwamnati a jihar a kan ta gudanar da bincike.
Sai dai wannan Dandali ya samu a wata majiya cewa, nan ba da dadewa ba ne ake sa ran kwamitin da ya gudanar da binkicen,karkashin wanda Chiromari ka jagoranta, zai sake tantance wasu daga cikin korarrun ma'aikatan domin dawo da su bakin aikinsu.
Dama dai tun da farko, gwamnatin ta jihar Yobe ta kuduri aniyar rage ma'aikatanta,wanda ta ce ta hakan ne za ta samun damar iya biyan mafi karancin albashin ma'aikata na N18,000.00 da gwamnatin tarayya ta amince da shi, al'amarin da wasu ke ganin cewa sallamar ma'aikatan ce gwamnatin ta somo.
No comments:
Post a Comment