Sunday, September 18, 2016

AN YI BARAN-BARAN TSAKANIN WANI DAN MAJALISA DA WASU JAGORORIN JAM'IYYARSA A JIHAR YOBE

Daga hagu, Hon. Shu'aibu Danladi Hamza, sai Alh. Auwalu Dogo


Bayanai na cewa, dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya Hon. Shu`aibu Danladi Hamza, ya raba gari da wasu kusoshin jam`iyyarsa ta APC, wadanda ake bayyana su a matsayin silar ci zabensa a shekara ta 2011 da 2015.

Shugaban matasan  jam`iyyar APC na karamar hukumar Nguru, Alh. Auwalu Dankwanyo, wanda aka fi sani da Auwal Dogo, tare da shugaban jam`iyyar  na yankin Hausari Alh. Auwalu Kiliya na daga cikin wadanda `yan sanda suka tsare domin amsa tambayoyi.

Shugabannin biyu dai na zargin Hon. Shu`aibu Danladi Hamza ne da hannu akan tsare su da `yan sandan suka yi a ranar Talatar da ta gabata a Gashu`a.

Ba a san dai ko menene dalilan dan majalisar na raba gari da wadannan jiga-jigai ba. Domin kokarin jin ta bakinsa da wannan Dandali ya yi ya cutura.

To sai dai kuma wannan Dandali, ya sami zantawa da daya daga cikin wadanda aka tsare Alh. Auwalu Dogo, wanda ke zargin dan majisar da hannu a kange su da `yan sandan suka yi har na sama da awoyi 7 ba tare da an saurare su ba.


Ga dai bayanin da Alh. Awal Dogo ya yi wa wannan Dandali:


`` … Gaskiya ne sha'aibu danladi hamza yayi duk abinda zaiyi wajen ganin anyi mana walakanci na karshe, ranar talata 13/09/2016 Mai martaba sarkin nguru ya gaiyace mu cin abinci no Auwalu dogo youths leader Nguru tare party chairman APC na Hausari auwalu kiliya, munzo kofar fada latti ana fitowa sai ga sha'aibu danladi tare da ari maidami chairman nguru sai auwalu kiliya yace hon yaya za ayi ahmadu mirwa yabawa duka party chairman na nguru out side 30k amma mu hudu na cikin gari ka hana mu laifin me mukayi maka kuma kabawa wasu wanda ma sun yakeka lokacin zabe, ana cikin haka sai aka fara ruwa sai nace kyaleshi kazo mu tafi ai zamu hadu, shikenan sai washe gari akaxo da hilux da yan sanda da bindiga aka kamamu akaje aka rufe mu a cell har tsawon awa bakwai sai Sen Ahmed Lawan yayi sannan aka fito damu misalin karfe 11.00 pm akace muje gobe mudawo. Tunda muka shiga hannun hukumar yan sanda baizo ba sai waya kawai yakeyi babu ruwansa damu da yanda ne. Wannan shine abinda yafaru ``.

Daga nan sai Auwal Dogo ya ci gaba da cewa `` ...Kuma yau (Asabar) munje area command na police gashua tun misalin 8.00am muna jira sai da karfe 2.00 pm akace wai muyi under taking babu mu babu shi, police suka rubuta undertaking akan babu ruwan mu dashi. wannan shine abinda yafaru ayau 17/09/2016. ``.

Wasu da wannan Dandali ya zanta da su a garin Nguru, na dora alhakin rabuwar kan dan majalisa Shu`aibu Danladi Hamza. Mutnen suka ce wananan butulci da abin kunya ne, duba da yadda a cewarsu, mutanen suka yi ruwa da tsaki domin ganin dan majilisar ya ci zabe a lokaci da ake yakin neman zabe, yayin da wasu ke ganin an yi gajen hakuri, da an kai zuciya nesa, a cewarsu da ba ta kai ga an yi hakan ba.

Wednesday, September 14, 2016

ASUU ZA TA TSINDIMA YAJIN AIKIN GARGADI A RAN 2 GA OKTOBA MAI ZUWA



Kungiyar malaman jami`o`i ta kasa ASUU, ta yi barazanar shiga yajin aikin gargadi daga ranar 2 ga watan Oktoba mai zuwa.

A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar a Litinin din nan mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na reshen jami`ar Abuja Mr. Ben Ugheoke, kungiyar ta ce gwamnatin tarayya ta gaza wajen sake komawa teburi tattaunawa da shgabannin kungiyar domin ganin an aiwatar da alkawuran da gwamnatin ta dauka a 2009 na inganta jami`o`in kasar.

Jaridar Premium Times ta nakalto jawabin yana cewa, ``mun yi kokarin ganin cewa gwamnati ta saurare mu, to amma sai muka fahimci cewa gwamnatin na wasa ne kawai da hankulanmu,  a saboda haka ne muka kudiri aniyar shiga yajin aikin gargadi na tsawo mako guda, daga ranar  2 ga watan Oktoban nan mai zuwa, domin  nunawa gwamnati cewan mu ba da wasa muke ba``.

Jawabin ya ci gaba da cewa, ``za mu shiga yajin aiki na sai baba ta gani, idan har gwamnati ta kasa yin wani abu na azo a gani bayan mun kamala yajin aikin gargadi ``.

Idan dai  za a iya tinawa,  a shekara ta 2009 ne gwamnatin tarayyar Najeriya, ta dauka wa uawar kungiyar ta ASSU wasu alkawuran inganta jami`o`in kasar, wanda kawo yanzu a cewa ASSUn, kasha 30 bisa 100 ne na alkawuran kawai gwamnatin ta aiwatar.



Monday, September 12, 2016

AN BUKACI MUSULMAI A KWANAKIN SALLAH DA SU DAGE DA ADDU`O`IN SAMUN SASSAUCIN KUNCIN RAYUWA



Kwamitin shari`a a Nguru jihar Yobe, ya yi kira ga al`umar Musulmai, da su himmatu cikin wadannan ranakun Sallah masu girma wajen yin addu`o`in neman sassauci daga Allah SWT, game da kuncin rayuwar da ake ciki.

A sako da ya rarraba zuwa ga masallatan Idi a Nguru, kwamitin ya kuma ja hankulan matasa dasu guji aikata munanan dabi`u da ka iya jefa su da al`uma cikin matsaloli a lokacin shagulgulan Sallah.

Da yake karanta sakon kwamitin a Litinin din nan bayan an idar da Sallah, limamin Masallacin Idi na Kwalejin Atiku Abubakar dake Nguru, Al-Sheikh Umar Jinjiri ya ce, tilas ne matasa su yi la`akari da halin da ake ciki wajen domin su kiyaye kansu daga aikata barna da ka iya janyo ta jefa al`uma cikin hadari
.
Da ma dai tun da farko, a daren jajiberen jiya Lahadi, mahukunta a garin Nguru suka bad a snarwar dakatar da zirga-zirgar abubuwan hawa, tun daga karfe 6:00 na safe har zuwa 4:00 na yamma.

Sunday, September 11, 2016

BARKA DA SALLAH DA FATAN ALLAH YA MAIMAITA MANA

Da fatan an yi Sallah lafiya

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu!

Dandalin Shu`aibu Abdullahi Sa`id Nguru, na taya daukacin al`umar Musulmi murnar babbar Sallah, da fatan za a ci gaba da shagulgulan  Sallah lami lafiya.

Da yake matasa su ne kashin bayan al`uma, wannan Dandali na jan hankalin matasan, da su yi karatun ta nutsu, wajen kauce wa aikata munanan dabi`u a lokutan bukukuwan Sallar.

Allah ya karbi ibadunmu, ya maimaita mana ta badin badada da rai da lafiya, amin.