Tuesday, August 11, 2020

Malaman Sakandare a Yobe sun shiga aji a karan farko bayan sake bude makarantu

Mafi yawancin daliban ajin karshe na makarantun karama da babbar Sakandare a jihar Yobe a yau Talata sun koma makarantunsu, inda a wasu makarantun har aka fara gabatar musu da darussa.

A Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar Yobe ta ba da izinin sake bude makarantun Sakandare domin daliban ajin kashe su dauki jarabawar karshe ta WASSCE.

Wakilin wannan Dandali a yau Talata ya kewaya wasu makarantu a Nguru, ya kuma ba da labarin cewa dalibai da dama sun koma, inda har a wasu makarantu aka gudanar da darussa.

A makarantar gwamnati ta Haya Islam inda wannan Dandali ya fara ziyarta, an martaba ka'idojin matakan kariya  da gwamnatin tarayya ta dingaya.

Wani Malamin makarantar da ya bukaci a boye sunansa a zantawarsa da wannan Dandali ya nuna jin daÉ—insa da bude makarantun.

Yana mai korafin cewa tsarin da a ka yi na bitar karatuttukan yaran a cunkushe yake.

A sauran makarantu ma a garin, wasu rahotanni sun nuna cewa lamarin bai sauya ba, yayin da a wasu kuma aka samu tsaiko kafin a gama gwajin zafin jikin dalibai.

A tuna cewa, a Litinin din mako mai zuwa 17 ga watan Agusta 2020 ne daliban makarantun Sakandare a fadin kasa za su fara daukar jarabawar karshe ta WASSEC da hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma WAEC ke shiryawa.

Saturday, August 08, 2020

Makarantu sun koma a jihar Yobe, malamai na ci gaba da tsara jadawalin duba masu daukar jarabawa

Malamai da daliban aji 3 na babbar Sakandaren kwana a jihar Yobe sun koma makarantunsu a yau Asabar.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta umarci makarantun Sakandare a jihar da su koma a ranakun 8 da kuma 11 ga watan Agusta 2020 domin tunkarar jarabawar WAEC ga daliban azuzuwan karshe.

A karamar hukumar Nguru a mafiya yawan makarantun daliban ba su koma ba tukunna.

Duk kuwa da cewa sanarwar da ma'aikatar ilimin jihar ta fitar a ranar Laraba ta nuna cewa makarantu masu zaman kansu za su koma ne a ranar Talatar 11 ga watan Agusta.

To sai dai an sami wasu makarantun Sakandare masu zaman kansu na Islamiyoyi a garin da suka koma tun a yau Asabar.

Wakilin wannan Dandali a yau Asabar ya ziyarci Makarantar Higher Islam ya kuma ba da labarin cewa dalibai kadan ne suka koma a yau Asabar, galibin wadanda suka koma su ne ma'aikata.

Malam Dahiru Usman Alfullaty, daya ne daga cikin Malaman da suka koma a yau Asabar, a zantawarsa da wannan Dandali ya bayyana cewa akwai tsirarun daliban da suka koma, amma galibinsu suna cikin kayan gida.

Ya kara da cewa a halin yanzu malamai sun dukufa wajen tsara jadawalin ajin karatu na musamman ga daliban da na masu dubu su a yayin da suke daukar jarabawarsu ta karshe da za fara mako mai zuwa.

Idan ba a manta ba Gwamnatin tarayya a kwanannan ta umarci daliban aji 3 na makarantun Sakandare a fadin kasa da su koma makarantunsu a ranar 4 ga watan Agusta, bayan sun shafe watanni 5 a gida, inda a jihar Yobe sai a Asabar din nan ce a ka bude makarantun.

Friday, August 07, 2020

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Yobe ta ba da gudumowar kayan kariya ga ma’aikatar ilimin jihar a gabanin sake bude makarantu

Kasa da awoyi 24 da a bude makarantu a jihar Yobe, Ma'aikatar ilimi Firamare da na Sakandare ta jihar ta karbi gudumowar kayan kariya daga annobar Corona daga ma'aikatar lafiya ta jihar.


Kayan kamar yadda ma'aikatar ilimin ta wallafa a shafinta na Facebook cikin wani jawabi a ranar Alhamis, za a yi amfani da su ne a makarantun da a ka bude.

Ma'aikatar ta ce ta karbi kimanin abubuwan wake hannu guda 100 da a ke sarrafasu da kafa, da mayukan tsaftace hannu na hand sanitizers.


Jawabin ya ambato cewa Sakataren dindindin na ma'aikatar lafiya ta jihar Alhaji Mahidu M. Alhaji tare  da Sakataren hukumar lafiya a matakin farko Dr. Babagana Kundi Machina ne suka mika kayan ga Kwamishinan Ma'aikatar ilimin Firamare da Sakataren jihar Dr. Muhammad Sani Idris tare da Sakataren dindindin na ma'aikatar Alhaji Yakubu Dokshi da sauran manyan jami'an ma'aikatar.

Thursday, August 06, 2020

Yobe za ta bude makarantu a ranar Asabar


Gwamnatin jihar Yobe ta sanar cewa za ta bude makarantu a ranar Asabar 8 ga watan Agusta.


Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandaren jihar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa daliban aji 3 na babbar Sakatare da daliban karamar Sakatare na makarantun kwana za su koma a ranar Asabar din 8 ga watan Agusta, yayin da daliban makarantu masu zaman kansu kuma za su koma a ranar Talatar 11 ga watan Agusta 2020.

Ma'aikatar a jawabin ta kuma shawarci daliban da su sanya takunkumin fuska. Tana mai shawartar hukumomin makarantun da su samar da matakan kariya game da annobar Covid-19

Kwamishinan ma'aikatar Dr. Muhammad Sani Idris ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni ta tabbatar da cewa a ko da yaushe za ta bi umarnin daukan matakan kariya da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Har wa yau kwamishinan ya bukaci daliban aji 3 na babbar Sakataren da su kintsa tsaf domin tunkarar jarabawar WAEC da za a fara a ranar 17 ga watan Agusta 2020 domin samun kyakkyawan sakamako ta yadda jihar za ta yi alfahari