Kasa da awoyi 24 da a bude makarantu a jihar Yobe, Ma'aikatar ilimi Firamare da na Sakandare ta jihar ta karbi gudumowar kayan kariya daga annobar Corona daga ma'aikatar lafiya ta jihar.
Kayan kamar yadda ma'aikatar ilimin ta wallafa a shafinta na Facebook cikin wani jawabi a ranar Alhamis, za a yi amfani da su ne a makarantun da a ka bude.
Ma'aikatar ta ce ta karbi kimanin abubuwan wake hannu guda 100 da a ke sarrafasu da kafa, da mayukan tsaftace hannu na hand sanitizers.
Jawabin ya ambato cewa Sakataren dindindin na ma'aikatar lafiya ta jihar Alhaji Mahidu M. Alhaji tare da Sakataren hukumar lafiya a matakin farko Dr. Babagana Kundi Machina ne suka mika kayan ga Kwamishinan Ma'aikatar ilimin Firamare da Sakataren jihar Dr. Muhammad Sani Idris tare da Sakataren dindindin na ma'aikatar Alhaji Yakubu Dokshi da sauran manyan jami'an ma'aikatar.




No comments:
Post a Comment