Friday, September 22, 2017

KUNGIYAR ‘YAN KABILAR IGBO TA NAJERIYA TA BUKACI ‘YAN KANO SU ZAUNA LAFIYA DA ‘YAN KABILAR TA IGBO



Kungiyar Ohaneze Indigbo tayi kira ga al’ummar Najeriya da su yi kokarin magance bambance-bambancen da ke tsakanin su, ta hanyar tattaunawa da juna, don tabbatar da Najeriya ta zama kasa daya dunkulalliya.

Shugaban kungiyar na kasa Chief John Nwodo ne yayi wannan kiran lokacin da ya jagoranci tawagar kungiyar, tare da wasu wakilan kabilar Ogbo zuwa fadar gwamnatin jihar Kano, a wani bangare na mika sakon zaman lafiya a jihohin Arewa.

Mista John Nwodo lokacin da yake jawabi ga mukaddashin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana cewa jihar Kano tana da al’ada na karbar baki ko daga ina suke hannu bibbiyu.

A cewar sa al’ummar kasar nan na kokarin manta tashin hankalin da ya faru a shekarar 1966, amma a yanzu wasu dai-dai kun mutane na kokarin tayar da hankalin al’umma.

Gidan Rediyo Freedom da ke Kanon ya rawaito cewa Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo na kasar ya lura da cewa akwai al’ummar kabilar Igbo da suka kai kimanin miliyan daya da dubu dari shida da ke zama a jihar Kano, tare da godewa al’ummar Kano bisa karamcin da suka bawa ‘yan kabilar ta Igbo.

Da yake jawabi, mukaddashin Gwamnan jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya shaidawa kungiyar ta Ohaneze Indigo cewa abinda yake damun ‘yan Arewa, shine rashin tsawatarwa matasan su da shugabannin kabilar Igbon suka gaza aiwatarwa, lokacin da ake ce-ce-kucen raba Najeriya.

Thursday, September 21, 2017

KUNGIYAR KWADAGO TA BAYYANA SUNAYEN JIHOHI 10 DA SUKA KI BIYAN ALBASHI GA MA’AIKATANTA



Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana sunayen jihohi goma wadanda ta ce sune kan gaba cikin jihohin da suka ki biyan ma’aikata bashin albashi da suke binsu duk kuwa da karbar makudan kudade da aka dawo musu dashi daga kungiyar bada lamuni ta Paris Club.

Kungiyar ta NLC kamar yadda Rediyo Freedom ya habarto ta kuma ce jihohin sun ki fitowa karara su bayyana yawan kudaden ceto tattalin arzikin jihohi da gwamnatin tarayya ta basu.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa Ayuba Wabba ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

Ya ce cikin jihohi Goman akwai shida wadanda lamarin su ya fi muni, yana mai buga misali da jihar Imo wanda ya ce har I zuwa yanzu ma’aikatan jihar suna karbar albashi ne kaso-kaso haka kuma jihar ta yi kememe ta ki bayyana adadin kudaden da ta karba daga kungiyar bada lamuni ta Paris Club da kudaden ceto tattalin arzikin jihohi da ta karba daga gwamnatin tarayya.

Ayuba Wabba ya kuma bayyana jihohin Bayelsa da Ondo da Ekiti da Benue da kuma Kogi da Osun da Ebonyi da Zamfara da kuma Abia a matsayin wadanda lamarin ya yi munin gaske.

Sunday, September 17, 2017

SARKIN KANO YA YI KIRA GA MATASA DA SU GUJI YIN AIKI DA JITA-JITA



Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya kirayi al’ummar arewacin Najeriya musamman matasa da su guji yin aiki da jita-jita da kaucewa amincewa da irin sakonnin da ake aikewa ta kafafen sadarwa na zamani wanda ka iya kaiwa ga harzuka hankulan jama’a.

Sarkin na Kano ya yi wannan jan hankali ne a ranar juma’ar da ta gabata lokacin da yake gudanar da hudubar sallar juma’a.

Malam Muhammadu Sanusi II ya ce ba ya kamata ga musulmi na kwarai daukar fansa akan wanda bai aikata masa laifin komi ba, kuma dukkanin kabilun da ke zaune a jihar Kano suna zaman amana ne, sannan addinin musulunci ya harmata a cutar dasu matukar basu tankawa kowa ba.

Haka kuma sarkin ya bukaci daukacin kabilun da suke zaune a nan birnin kano da su zauna lafiya kuma kada su shigar da kawunansu cikin rigima, inda ya ce yin hakan zai haifar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar nan.

A karshe mai martaba sarkin ya bukaci limamai da sauran masu fada a ji a jihar Kano su ci-gaba da jan hankalin matasa a arewacin kasar su zauna lafiya da wadanda suke tare dasu domin kare mutuncin su da martabar addinin musulunci.

Saturday, September 16, 2017

GWAMNONIN JIHOHIN KUDU MASO GABASHIN NAJERIYA SUN YI TUR DA KUNGIYAR FAFUTUKAR KAFA KASAR BIAFRA


Daukacin gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun yi tur tare da haramta irin ayyukkan da kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB ke yi a yankin kudancin kasar.

Shugaban kungiyar Gwamnonin kuma gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ne ya sanar da hakan bayan kammala wata ganawar sirri da gwamnoni suka yi da shugabanin al’ummar kabilar Igbo da sauran masu ruwa da tsaki a fadar gwamnati da ke Enugu.

Gidan Rediyon Freedom da ke Kano ya rawaito cewa Gwamnonin sun kuma yi kira ga shugabanin kunigiyar da saura dukkanin wasu fusatattun kungiyoyo a yankin da su ayyana bukatunsu su kuma aike dasu zuwa kwamitin gwamnoni na zauren majalisar dokokin kasar nan, da kuma kungiyar Al’ummar Igbo ta Ohaneze, da zauren majalisar kasar nan karkashin shugan kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin kasar nan.

Haka kuma gwamnonin sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye sojojin da aka jibge a yankin inda suka bukaci a bar yan sanda da su ci gaba da ayyukan kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Gwamnoni dai da suka kunshi jahohi biyar sun tsai da wannan matsaya ne a wata ganawar sirri na awanni biyar da suka gudanar a fadar gwamnatin jihar Enugu wanda ya samu halartar mataimakin shugaban majalisar dattijawa Ike Ekweremadu, da shugaban kunigyar alummar Igbo ta Ohanaeze John Nwodo da kuma babban kwamandan sojin kasar nan mai lura da bataliya ta 83 laftan janar Adamu Abubakar.

Wednesday, September 13, 2017

GWAMNATIN SAUDIYYA TA YANKEWA WANI MAHAJJACI DAN JIHAR SOKOTO WATANNIN UKU A GIDAN YARI


Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zaman ta a kasar Saudiyya ta yanke wa wani mahajjaci Mallam Mamman Kwa-Kwazo hukuncin zaman Gidan kaso har na tsawon watanni uku.

Malam Mamman wanda dan asalin karamar hukumar Goronyo ne da ke jihar Sokoto, gwamnatin kasar ta same shi da lafin yin karya da mallakar wata jakar kudi da aka tsinta wadda kuma ba tashi ba ce.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin sakataren karamar hukumar Goronyo Lawal 'Yar-Tsakuwa, cewa ya yi, mahajjacin ya tsinci jakar kudin ne a harabar masallacin a ranar juma’a da ta gabata.

Rahotannin sun ce Mallam Mamman Kwa-kwazo tun da fari yaki amincewa ya bayar da jakar kudin ga mamallakinta, wanda hakan ne ya sanya aka garzaya da shi ga jami’an tsaro.

A cewar Sakataren ba a san inda bakon Gidan yarin ya fito ba, sai daga baya ne aka mika shi sansanin mahajjatan jihar Sokoton, bayan an tabbatar da cewa daga karamar hukumar da ta fito daga yankin yake, yanzu haka dai gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatar da Mamman Kwa-kwazo shiga kasar har na tsawon watanni biyar.

Thursday, September 07, 2017

AN BUKACI GWAMNATIN JIHAR YOBE DA TA SAMAR DA KANANAN TASHOSHIN FM A SHIYYOYI 3 NA JIHAR



An yi kira ga gwamnatin jihar Yobe da ta kafa karamar tashar rediyo mai watsa shirye-shirye ta zangon FM a kowace shiyya cikin shiyyoyi uku na jihar.

Wani ma'abocin sauraren radiyo Malam Ibrahim Muhd shi ya yi wannan kiran yayin zantawarsa da wannan Dandali ranar Alhamis a garin Nguru.

Malam Ibrahim Muhammad wanda ya shafe shekaru sama da talatin yana sauraren rediyo, ya ce akwai bukatar gwamnati ta wadatar da jihar da kafofin sadarwa musamman ma gidajen rediyo.

Ya ce fa'idar kafa irin wadannan tashoshin a bayyane take duba da yadda al'umomi a wannan zamani suka raja'a wajen sauraran rediyo.

Ya kara da cewa tashoshin za su taimaka wajen sauraren Rediyon jiha wanda yanzu haka ke yi wa wasu garuruwan jihar wuyar kamawa musamman garuruwan arewacin jihar.
 
A don haka sai ya bukaci gwamnatin da ta kafa rediyon shiyya (zonal Radio) a shiyyoyi ukun da suka hada da Gabaci, da Kudanci da kuma Arewacin Yobe, ta yadda sadarwa za ta saukaka a shiyyoyin da ma jihar baki daya.

Yana mai kwatanta rediyoyin a matsayin wata hanya da gwamnati da alumomi za su iya cin gajiyarsu ta fuskoki daban-daban a fadin jihar baki daya.

Saturday, September 02, 2017

NCC TA GARGADI ‘YAN NAJERIYA KAN AMFANI DA WAYOYIN JABU



Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, ta gargadi ‘yan Najeriya game da yin amfani da wayoyin salula na jabu, tare da cewar yawan amfani da su na daya daga cikin abin da ke jawo wasu nau’ika na cutar daji wato Cancer.

Wani jami’in hukumar Kunle Olorundare ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani tare da masu ruwa da tsaki, wanda hukumar ta NCC da ke shiyyar Ibadan ta shirya.

Gidan Rediyon Freedom da ke Kano ya ambato Mista Olorundare yana cewa, ya lura da cewa wayoyin salula na jabu sun samu karbuwa a fadin kasar nan, kuma yin amfani da su wata babbar barazana ce ga rayuwar al’umma.

Ya kara da cewa ire-iren wadannan wayoyin na daya daga cikin abinda ke sabbaba matasalar ayyukan sadarwa, inda yace hukumar ta NCC zata dauki mataki kan masu dillancin wayoyin na jabu.

Olorundareya kuma bukaci masu dillancin wayoyin nasalula a fadin kasar nan da su tabbatar da cewa hukumar ta amince da ingancin wayoyin da suke siya daga hannun abokan huldar su.