Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana sunayen jihohi goma wadanda ta ce sune kan gaba cikin jihohin da suka ki biyan ma’aikata bashin albashi da suke binsu duk kuwa da karbar makudan kudade da aka dawo musu dashi daga kungiyar bada lamuni ta Paris Club.
Kungiyar ta NLC kamar yadda Rediyo Freedom ya habarto ta kuma ce jihohin sun ki fitowa karara su bayyana yawan kudaden ceto tattalin arzikin jihohi da gwamnatin tarayya ta basu.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa Ayuba Wabba ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.
Ya ce cikin jihohi Goman akwai shida wadanda lamarin su ya fi muni, yana mai buga misali da jihar Imo wanda ya ce har I zuwa yanzu ma’aikatan jihar suna karbar albashi ne kaso-kaso haka kuma jihar ta yi kememe ta ki bayyana adadin kudaden da ta karba daga kungiyar bada lamuni ta Paris Club da kudaden ceto tattalin arzikin jihohi da ta karba daga gwamnatin tarayya.
Ayuba Wabba ya kuma bayyana jihohin Bayelsa da Ondo da Ekiti da Benue da kuma Kogi da Osun da Ebonyi da Zamfara da kuma Abia a matsayin wadanda lamarin ya yi munin gaske.

No comments:
Post a Comment