Friday, September 22, 2017

KUNGIYAR ‘YAN KABILAR IGBO TA NAJERIYA TA BUKACI ‘YAN KANO SU ZAUNA LAFIYA DA ‘YAN KABILAR TA IGBO



Kungiyar Ohaneze Indigbo tayi kira ga al’ummar Najeriya da su yi kokarin magance bambance-bambancen da ke tsakanin su, ta hanyar tattaunawa da juna, don tabbatar da Najeriya ta zama kasa daya dunkulalliya.

Shugaban kungiyar na kasa Chief John Nwodo ne yayi wannan kiran lokacin da ya jagoranci tawagar kungiyar, tare da wasu wakilan kabilar Ogbo zuwa fadar gwamnatin jihar Kano, a wani bangare na mika sakon zaman lafiya a jihohin Arewa.

Mista John Nwodo lokacin da yake jawabi ga mukaddashin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana cewa jihar Kano tana da al’ada na karbar baki ko daga ina suke hannu bibbiyu.

A cewar sa al’ummar kasar nan na kokarin manta tashin hankalin da ya faru a shekarar 1966, amma a yanzu wasu dai-dai kun mutane na kokarin tayar da hankalin al’umma.

Gidan Rediyo Freedom da ke Kanon ya rawaito cewa Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo na kasar ya lura da cewa akwai al’ummar kabilar Igbo da suka kai kimanin miliyan daya da dubu dari shida da ke zama a jihar Kano, tare da godewa al’ummar Kano bisa karamcin da suka bawa ‘yan kabilar ta Igbo.

Da yake jawabi, mukaddashin Gwamnan jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya shaidawa kungiyar ta Ohaneze Indigo cewa abinda yake damun ‘yan Arewa, shine rashin tsawatarwa matasan su da shugabannin kabilar Igbon suka gaza aiwatarwa, lokacin da ake ce-ce-kucen raba Najeriya.

No comments:

Post a Comment