Mutane da dama ne a jihar Yobe ke ci gaba da yin kiraye-kiraye ga gwamnati da ta yi wa Allah ta cika musu alkawarin dawo da sufurin mashina a fadin jihar wanda ta dauka kusan shekaru uku (3) da suka gabata.
Wannan tunatarwa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da yin ikirarin samun zaman lafiya, tare da bayyana nasarar fatattakar mayakan Boko Haram.
Mutanen sun kuma sha alwashin sadaukar da kansu ga gwamnatin a ranar zabe muddun gwamnatin ta cika wannan alkawari da ta dauka.
Wani Magidanci a garin Nguru Malam Musa Kalla ya fada a zantawarsa da wannan Dandali ranar Laraba cewa, akwai bukatar gwamnati ta dawo da zirga-zirgar mashina ko da kuwa ta mutum dai-dai ce duba da yadda ake kara samun kyautatuwar zaman lafiya da kuma yadda ake fama da matsin rayuwa.
Malam Kalla ya ce dawo da zirga-zirgar mashinan zata taimaka wajen bunkasa fannin noma da fannin ma'aikatun gwamnati, tare da rage zaman kashe wando da dai sauransu.
Tun da farko a zantawarsa da wannan Dandali, wani Malami da ya ce a boye sunansa ya yaba wa gwamnatin ne game da namijin kokarin da take na inganta aiki da kuma ma'aikata, da ma kokarinta na sauya fasalin jihar baki daya.
To sai dai kuma Malamin ya koka akan irin makudan kudaden da ya ce suna batarwa domin zuwa wuraren ayyukansu masu nisa sakamakon rashin sauwakakken abin hawa.
A don haka ne ma sai ya yi kira ga gwamnatin da ta taimaka musu ta hanyar dawo da sufirin mashina ko da na mutum daya ne kamar yadda ta alkawarta a baya.
Ya ci gaba da cewa hakan zai taimaka musu wajen sauke nauyin da aka dora musu da gaskiya ba tare da yin lalaci ba.
"A shekarun baya da suka shude mu ma ba za mu amince da dawo da mashinan ba, duba da yadda a lokacin babu wanzazzen zaman lafiya, amma yanzu Alhamdulillah zaman lafiya ya samu". In ji Malamin.
Idan ba a manta ba, a gabanin zaben 2015, gwamnatin jihar Yobe ta fada ta bakin kakakin gwamnan jihar Malam Abdullahi Begu a wata hira da BBC Hausa cewa, gwamnatin ba da dadewa ba zata dawo da zirga- zirgar mashina na mutum dai-dai a fadin jihar, almarin da har yanzu shiru kamar an shuka dusa.

No comments:
Post a Comment