Sunday, March 11, 2018

Ya kamata a katange Makarantar Higher Islam da ke Nguru ko don saboda tsaro — I. A Nguru

An yi kira ga Gwamnan jihar Yobe Alh. Ibrahim Gaidam da ya hanzarta waiwayar Makarantar Higher Islam da ke Nguru a aikin da ya somo na kwaskware makarantun sakandaren kwana na jihar. 

Wani uba a Nguru Malam Ibrahim Alaramma shi ya yi wannan kiran yayin zantawarsa da wannan Dandali ranar Lahadi a Nguru.

Wannan kiran na zuwa ne makonni kadan da sace 'yan mata 110 daga makarantar sakandaren 'yan mata ta garin Dapchi a jihar da ake zargin Boko Haram da aikatawa.

Alaramma ya ce yana mamakin yadda mai girma Gwamna ya yi kamar ya manta da makarantar, wacce ta yaye manyan mutane masu yawa da suka fantsama ciki da wajen kasa.

Ya kara da cewa a halin yanzu haka ba ya tsammanin akwai Makarantar sakandaren da ta kai ta yawan dalibai a fadin jihar naki daya.

A cewarsa to amma sai dai an bar makarantar a yashe.

Ya ci gaba da cewa, al'amarin da gaske yana ba shi mamaki a yadda ya san Gwamnan wajen kokarinsa na farfado da harkar ilimi, amma kuma ko ta yaya aka bar daruruwan dalibai a filin Allah? Filin da a cewarsa babu ko danga ballantana katanga.

A don haka sai ya bukaci Gwamna Gaidam da yi duk mai yiwuwa wajen ganin an katange Higher Islam din, tare da gina mata sabbin azuzuwa da dakunan kwanan dalibai da na malamai cikin lokacin da ba mai nisa ba.

Yana mai siffanta yin hakan a matsayin wani babban kandagarki da zai taimaka wajen kare makarantun sakandaren jihar daga farmakin 'yan ta'adda.

No comments:

Post a Comment