Friday, June 15, 2018

Kokarin nemo aibin Musulmi da yayata shi ba ya daga koyarwar Muslumci — Hudubar Juma'a

An yi kira ga al'umar Musulmai da su zama masu rufe asirin 'yan uwansu domin ribatar rayuwar duniya da ta lahira.  

Babban limamin masallacin Juma'a na Kwalejin Atiku Abubakar da ke Nguru Al-sheikh Umar Jinjiri wanda aka fi sani da Iya da Baba, shi ne ya yi wannan kiran a hudubarsa ta Sallar Juma'a yau a garin Nguru.

Sheikh Iya da Baba ya ce akwai bukatar Musulmai da su rungumi al'adar nan ta sakaye sirrin junansu musamman ma ga abubuwan da ka iya ragewa juna kima.

Malamin a hudubar tasa ya kuma gargadi Musulman da su nisantar da kansu kacokan wajen binciko sirrin dan uwansu da Allah ya rufe tare da kokarin yayata shi.

Yana mai cewa yin hakan ita ce karantarwar addinin ga Musulmai.

Malamin daga karshe ya rufe da Hadisin Manzon Allah ( SAW), inda ya bukaci manya daga cikin Musulmai su tausawa kananansu, yayin da kananan su kuma su girmama wadanda suka fisu yawan shekaru.

No comments:

Post a Comment