Sunday, June 30, 2019

MU MUKA SA KANMU AIKIN GAYYA BA WANI NE YA SAKA MU BA

Matasa na kan aikin yashe magudanan ruwa a Bulabulin Nguru

Wasu matasa a Bulabulin Nguru da suka gudanar da aikin yashe magudanan ruwa a yau Lahadi sun musanta cewa wai saka su aka yi domin su yashe magudanan ruwa a wasu sassan unguwar.

Matasan sun karyata bayanan ne biyo bayan abin da suka kwatanta da farfaganda da wasu suke yadawa a kafafen sada zumunta kan cewa wai mahunkuntan gari ne suka umarci da a gudanar da aikin.

A zantawarsu da Wannan Dandali a yau Lahadi jim kadan bayan sun kammala aikin yau da suka somo shi ta magudanan ruwan titin Zakariya Mai malari (Layin Marigayi Haruna Pharmacy ko ko layin Abdulhamidi ko na marigayi Alh. Ari Machina), matasan suka ce za su ci gaba gobe idan Allah ya kai mu ta layin Alh. Kwalle inda suke sa ran danganawa da layin Alh. Adam mai mota.

Shugaban masu gudanar da aikin da ya bukaci a boye sunansa ya ce duk shekara sun saba gudanar da Wannan aiki, kuma rashin adalci ne a ce wasu ne suka saka a a yi aikin a yanzu.

Ya ce bai sani ba ko a wani wuri, amma su dai domin radin kansu suka gudanar da aikin.

Daya daga cikin masu aikin kuma na hannun damar Hon. Lawan Sani, Musa Mati wanda aka fi sani da Musa kafar yawo ya shaida wa Wannan Dandali cewa aikin na ganin damarsu ne bai wai umarni ne na mahunkuntan gari ba.

Ya ce babu azzalimi kamar wanda ya alakanta aikinsu da umarnin mahunkunta.

Tunda farko Hon. Lawan Sani dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya a jiya Asabar ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook inda yake gayyatar magoya bayansa da su fito a gobe Litinin da misalin 6:00 na safe domin sanya tubalin aikin yashe magudanan ruwan da za a somo daga arewacin garin Nguru.

Friday, June 28, 2019

Mun gamsu Mai Mala Buni alheri ne — wasu ma'aikata a jihar Yobe

Gwamna Buni na jihar Yobe

Wasu a ma'aikata a jihar Yobe sun bayyana cewa izuwa yanzu zuciyarsu ta sami nutsuwa da sabon gwamnan jihar Mai Mala Buni.

Ma'aikatan sun bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin zantawarsu da wannan Dandali a Nguru.

Suka ce sun yi mamakin yadda gwamna Buni ya biya su albashin watan Juni tun da wurwuri.

Wani ma'aikaci a mataki na jiha ya fada a zantawarssa da wannan Dandali cewa a zatonsa albashi sai baba ta gani, duba da cewa a mafi yawan lokuta idan aka sami canjin jagora akan yi wasu sabbin tsare-tsare kafin komai ya dawo daidai.

" to sai ga shi ba zato ba tsammani da sanyin safiya albashi ya iso tun a ran 25 ga wannan wata" a cewar ma'aikacin.

Shi ma wani ma'aikacin da ya zanta da wannan Dandalin a Nguru gode wa Gwamnan ya yi inda ya kwatanta shi da cewa alheri ne.

Ya kuma ya ba da yadda gwamna ya sassauta dokar takaita zirga-zirga( Curfew) domin 'ya'yan jihar su sake samun sa'ida.

An rantsar da Mai Mala Buni a ranar 29 ga watan Mayun 2019 a bayan Ibrahim Gaidam ya kammala zagonsa na biyu.

Sunday, June 23, 2019

SUKAR SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR NGURU DA HON. LAWAN SANI YA YI CI GABAN DIMUKRADIYYA NE A GARIN NGURU— Masu fashin bakin siyasa


An kwatanta kalaman Hon. Lawan Sani da ya yi kan shugaban karamar hukumar Hon. Ali Maidami a matsayin girman Dimukradiyyar garin Nguru

Wasu masu fashin bakin siyasa a garin Nguru sun bayyana cewa kalaman Hon Lawan Sani da ya yi akan shugaban karamar hukumar Nguru a ranar Laraba wata babbar alama ce dake nuna girman Dimukradiyyar garin Nguru.

Wani da ya ga siyasar jiya kuma yake ganin ta yau da ya zanta da wannan Dandali a Lahadin nan ya ce abin da dan majalisar ya yi ba abu ne sabo a Dimukradiyya ba.

Masanin siyasar da ya ce a boye sunansa saboda wasu dalilai na kashin kansa ya jadda cewa abu ne mawuyaci wasu su fahimci muhimmancin hakan, musamman ma wadanda suke fushi da fushin wani.

Ya ce  kalaman Lawan Sani abin a yaba ne ba abin yin cecekuce ba.

Ya kara da cewa idan aka dubi jihohin da siyasarsu ta ci gaba, to fa za a samu cewa 'yan siyasar wadannan jihohi na ci gaba da kalubalantar juna.

Ya ce ya yi matukar mamakin yadda ya ga wasu da ya kwatanta da 'yan tashi biya suna ta kunfar baki maimakon su dubi abin duba na tsanaki da hangen nesa musamman kan zarge-zargen da dan majalisar ya yi akan shugaban.

Yana mai buga misali da jihar Kano inda a cewarsa ba ma a mabambanta jam'iyyu ba, ya ce akan sami irin hakan har a tsakanin 'yan jam'iyya guda wani ya soki wani.

Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata ne Hon. Lawan Sani a shafinsa na Facebook ya kalubalanci shugaban kan zargin cewa shugaban na shirin gwanjatar da ruwan kogin Nguru, zargin da shugaban ya musanta.

Wakilin wannan Dandali ya aike wa shugaban karamar hukumar da sako a shafinsa na Facebook don jin ko ina aka kwana game da wannan zargi, to amma sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton shugaban bai ce da shi komai ba.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gungun masunta ne a garin suka nemi taimakon dan majalisar da ya sa baki domin ganin an dakatar da zargin gwanjatar da ruwan kogin Nguru da ake yi wa shugaban kan zargin cewa wai masuntan ba su zabi dan majalisar jiha na Jam'iyyar APC ba Hon. Shuaibu Danladi Hamza da ya kasa kai bantensa a zabukan da suka gabata.

Hon. Lawan Sani dai shi ne dan majalisar jiha daga Nguru tsakiya a jam'iyyar PDP mai adawa yayin da shugaban karamar hukumar Nguru Hon. Ali Maidami kuma dan jam'iyyar APC ne mai mulki.

Friday, June 21, 2019

Wani limami a Nguru da ya shahara wajen yin addu'a ga shugaban kasa Buhari ya daina yin addu'o'in inda ya canja zuwa kan 'yan kasa.


Bayanai sun nuna cewa wasu da suke bibiyar hudubobin malamin sun gano cewa a baya babu yadda za a yi Sheshin Malamin ya tsallake shugaban cikin addu'o'i.

Wasu da suka zanta da Wannan sun tabbatar da cewa sun kasa kunne a yayin da malamin ke gabatar da hudubar Sallar Idin da ya gabata, to amma sai dai ba su ji malamin ya ambato shugaban kasa a addu'o'i kamar yadda ya saba a baya ba.

Daga nan a cewarsu sai suka fara zargin cewa ko malamin ya dawo daga rakiyar shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wakilin wannan Dandali a yau Juma'a ya ziyarci Masallacin da sheshin Malamin yake limanci domin gudanar da Sallar Juma'a, ya kuma tabbatar da cewa malamin ya tsallake shugaban kasa a addu'o'in da ya saba, wanda a maimakon hakan sai ya karkata kan yin addu'o'i ga talakawan kasa.

Duk kuwa da cewa Malamin ba shi ne ya sanar da daina yi wa shugaban addu'a ba, to amma sai dai an gano hakan ne tun a hudubarsa ta Sallar Idin da ya gabata.

A kan haka ne ma wakilin wannan Dandalin ya yi kokarin jin martanin Sheshin Malamin da ake yi wa take da( Na-Buhari mai 'yan addu'o'i), to amma sai dai wakilin Dandalin bai yi gam da katar ba.

NEXT LEVEL!

Wednesday, June 19, 2019

An fara nuna wa juna yatsa tsakanin Dan majalisa Hon. Lawan Sani da shugaban karamar hukumar Nguru Hon. Ali Maidami



Wannan na zuwa ne tun bayan bayyanar wani sako da Hon. Lawan Sani Inuwa dan majalisar jiha na kwaryar Nguru mai jiran gado ya rubuta a ranar Laraba a shafinsa na Facebook,  inda yake kalubalantar Hon. Ali Maidami shugaban karamar hukumar Nguru.

Duk kuwa da cewa Hon. Lawan Sani bai fito fili ya bayyana ko kan menene yake sukan shugaban ba, to amma sai dai ya kwatanta shugaban karamar hukumar da mai son tada zaune tsaye.

A sakon kazalika Hon. Lawan Sani ya kuma zargi Shugaban da yunkurin jefa matasa zaman kashe wando, tare da raba kawunan jama'a.

To sai dai a martaninsa da yammacin Larabar nan wanda Lawan Aljan Nguru ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shugaban karamar hukumar Nguru Hon. Ali Maidami ya karyata daukacin zargin dan majalisar.

Yana mai cewa zarge-zargen  ba su da tushe ballantana makama.

To sai dai a 'yan kwanakin nan an sami jita-jitar cewa akwai takaddamar da ta taso tsakanin masunta a garin da mahukuntan karamar hukumar kan batun cinikin ruwan kogi kafin masuntan su yi sun kifi a kogin Nguru.

Jita-Jitar ta ce za a siyar wa masuntan ruwan kogin ne kan farashin kudi N500,000 kuma wai an saya N200,000 amma an ce da su albarka.

Jita-Jitar ta kuma alakatanta sayar da kogin da zargin cewa wai masuntan ba su zabi jam'iyyar APC ba a zabubnukan da suka gabata.

To ko ma dai yaya ne? wannan Dandali ya yi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar kan wannan jita-jitar to amma sai dai hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba.

Wasu masu fashin bakin siyasa a Nguru sun bayyana cewa wannan wata 'yar manuniya ce dake nuna cewa Dimukradiyyar garin ta fara girma.

Hon. Lawan Sani dai dan jam'iyyar adawa ce ta PDP dake wakiltar Nguru ta tsakiya a Majalisar jiha yayin da Hon. Ali Maidami kuma dan jam'iyyar APC mai mulki ne.