Sunday, June 23, 2019

SUKAR SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR NGURU DA HON. LAWAN SANI YA YI CI GABAN DIMUKRADIYYA NE A GARIN NGURU— Masu fashin bakin siyasa


An kwatanta kalaman Hon. Lawan Sani da ya yi kan shugaban karamar hukumar Hon. Ali Maidami a matsayin girman Dimukradiyyar garin Nguru

Wasu masu fashin bakin siyasa a garin Nguru sun bayyana cewa kalaman Hon Lawan Sani da ya yi akan shugaban karamar hukumar Nguru a ranar Laraba wata babbar alama ce dake nuna girman Dimukradiyyar garin Nguru.

Wani da ya ga siyasar jiya kuma yake ganin ta yau da ya zanta da wannan Dandali a Lahadin nan ya ce abin da dan majalisar ya yi ba abu ne sabo a Dimukradiyya ba.

Masanin siyasar da ya ce a boye sunansa saboda wasu dalilai na kashin kansa ya jadda cewa abu ne mawuyaci wasu su fahimci muhimmancin hakan, musamman ma wadanda suke fushi da fushin wani.

Ya ce  kalaman Lawan Sani abin a yaba ne ba abin yin cecekuce ba.

Ya kara da cewa idan aka dubi jihohin da siyasarsu ta ci gaba, to fa za a samu cewa 'yan siyasar wadannan jihohi na ci gaba da kalubalantar juna.

Ya ce ya yi matukar mamakin yadda ya ga wasu da ya kwatanta da 'yan tashi biya suna ta kunfar baki maimakon su dubi abin duba na tsanaki da hangen nesa musamman kan zarge-zargen da dan majalisar ya yi akan shugaban.

Yana mai buga misali da jihar Kano inda a cewarsa ba ma a mabambanta jam'iyyu ba, ya ce akan sami irin hakan har a tsakanin 'yan jam'iyya guda wani ya soki wani.

Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata ne Hon. Lawan Sani a shafinsa na Facebook ya kalubalanci shugaban kan zargin cewa shugaban na shirin gwanjatar da ruwan kogin Nguru, zargin da shugaban ya musanta.

Wakilin wannan Dandali ya aike wa shugaban karamar hukumar da sako a shafinsa na Facebook don jin ko ina aka kwana game da wannan zargi, to amma sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton shugaban bai ce da shi komai ba.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa wasu gungun masunta ne a garin suka nemi taimakon dan majalisar da ya sa baki domin ganin an dakatar da zargin gwanjatar da ruwan kogin Nguru da ake yi wa shugaban kan zargin cewa wai masuntan ba su zabi dan majalisar jiha na Jam'iyyar APC ba Hon. Shuaibu Danladi Hamza da ya kasa kai bantensa a zabukan da suka gabata.

Hon. Lawan Sani dai shi ne dan majalisar jiha daga Nguru tsakiya a jam'iyyar PDP mai adawa yayin da shugaban karamar hukumar Nguru Hon. Ali Maidami kuma dan jam'iyyar APC ne mai mulki.

No comments:

Post a Comment