Wednesday, December 14, 2016

ANWARUL ISLAM NGURU: Bikin bankwana da dalibai masu koyon aikin Malanta


Bikin bankwana da dalibai masu koyon dabarun koyarwa

Makarantar Sakandaren Anwarul Islam Nguru, ta gudanar da bikin bankwana da dalibai masu koyon aikin malanta da aka turo makarantar a watan Oktoban da ya wuce.

Dalibai 11 ne daga sashe daban-daban na Kwalejin Shari'a da darrusan Muslumci ta Atiku Abubakar Nguru suka zo makarantar ta Anwarul Islam domin koyon aikin malantan da sai a Larabar nan ce suke karkare shi.

Bikin da aka gudanar da marecen Laraban nan a harabar Makarantar dake unguwar Bulabulin Nguru, an shafe awowi ana gudanar da shirye-shirye daban-daban a cikinsa.

An gudanar da gasa a darrusan daban-daban cikin Muslumci da harsunan Larabci da Turanci da Hausa, da fannin na'ura mai kwakwalwa, da kimiya da fasaha da dai sauransu.

Dalibai da suka yi nasara a gasar da aka shirya an ba su kyauttuka a wurin taron.

A bangare guda kuma, an gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin, inda shugaban Makarantar Malam Muhammad Kabir Ali, a jawabinsa ya gode wa daliban da aka turo musu kan jajircewar da suka nuna wajen shiga aji don ganin sun koyar da yara matuka.

Su ma dai daliban da aka turo a jawabinsu godiyarsu ce suka nuna ga hukumomi da daliban makaranta, tare da naiman afuwa daga gare su bisa wani kuskure da suka ce idan har sun yi.

Da yake magana a madadin sauran daliban, dalibi mai sanin makamar malanta Umar Alhasan, ya ce suna takaicin rabuwarsu da Anwarul Islam matuka.

Daliban sun kunshi Abdullahi Abdullahi Rabi'u, da Auwal Muhd Musa, da Adamu Lawan, da Aisha Usman Bala, da Aisha Dahiru, da Amina Muhd Harun.

Sauran sun hada da, Hafsa Ibrahim Umar, da Hamisu Salisu Musa, da Idris Adamu, da kuma Rashida Abdullahi.

Bikin dai ya sami halartar jama'a da dama daga ciki da wajen makaranta.

Sunday, December 11, 2016

DA GANGAN PHCN SUKE KIN BAYAR DA WUTA A GARIN NGURU - Mazauna gari




Wasu mazauna garin Nguru a jihar Yobe, sun zargi hukumar ba da hasken wutar lantarki a garin PHCN da cewa da gangan suke kin barin wuta ta jima idan an kawo.

Wannan zargin na zuwa ne a Lahadin nan, wuni na uku da aka shiga cikin wadatacciyar wutar lantarki a garin da aka sake ta tun ranar Juma'a.

Wasu da wannan Dandali ya zanta da su a Nguru sun bayyana cewa, hukumar ta PHCN ta bar wutar ne a garin don kawai jin dadin wani mutum guda daya.

Suka ce a baya hukumar ta PHCN ta sha yaudararsu da cewa matsaloli ne na rashin ingantattun kayan aiki, su suka sa wutar take kin zama idan an kawo.

Malam Abubakar Sadik Bello, wani mazaunin Nguru ne dake amfani da wutar lantarki, ya ce yanzu dai ta tabbata karya ce a sake ce da mu wai rashin ingantaccen kayan aiki ne ke sa wa ba ma jimawa da wuta.

Ya kara da cewa a baya filashin suke yi mana, yanzun kuma da sun dauke da sun dawo da ita, kuma idan suka dawo da ita sai ta dade.

"kowa ya sani buki da ake a gidan Alh. Balarabe Abdullahi Nguru, shi ne ya sa aka bar wuta a gari". A cewarsa.

Shi ma dai wani mai cajin waya a Nguru Hasan Muahammad cewa ya yi, an sako wutar ce kawai saboda bikin gidan Balarabe Dj.

Kazalaka mutanen Sun kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a lamarin samar da wutar lantarki a garin da su dubi lamarin domin gano mecece matsalar da ake ta cewa ita ta hana zaman wuta.

To ko ma dai yaya ne? Wannan Dandali ya yi kokarin jin ta bakin jami'an hukumar ta PHCN domin jin martaninsu akan wannan zargi, to amma sai dai hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba.

Idan ba a manta ba dai, Alhajin dan kasuwa Balarabe Abdullahi Nguru ko Balarabe Dj, shi ne ya yi aikin sabunta wutar lantarki da aka kammala kwannan a daga Kano - Nguru, wadda wasu ke ganin gara jiya da yau ta fuskar tsayuwar wuta. Yayin da wasu kuma ke ganin aikin ya yi nasara.

Samun tsayayyiyar wutar lantarki a Nguru na wuni ukun da suka zo daidai da lokutan da ake shagulgulan biki a gidan hamshakin dan kasuwa Balarabe Dj dai, ya jefa shakku a zukatan wasu mazauna garin game da sahihancin zantuttukan hukumar PHCN na rashin tsayuwar wuta a garin Nguru.

Yanzun dai kallo ya koma sama, inda mutane suka zuba ido don ganin shin ko da gaske ne wutar za ta dore? Ko kuma dai hukumar ta PHCN za ta gaskata wannan zargi.

Monday, December 05, 2016

SUKAR GWAMNATIN BUHARI GYARA KAYANKA NE - BBC Hausa



A Najeriya, masu sharhi sun fara tsokaci kan sukar da fadar shugaban kasar ke fuskanta daga wasu muhimman mutane a kasar, wadanda a baya suka kasance cikin masu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.

Suka na baya-bayan na dai ya fito ne daga Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II wanda ya soki manufofin gwamnati na tattalin arziki.

A baya ma wasu rahotanni sun ambato tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo yana nuna takaicinsa a kan yadda al'amura ke tafiya a kasar.

Dr. Abubakar Kari malami ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja, ya ce baya ga wasu masu fada aji da ke sukar gwamnati, akwai talakawa da dama dake korafi kan yadda gwamnati ke tafiya.

Ya kara da cewa talakawa sun zabi Muhammadu Buhari ne domin ya magance matsalolin da suka addabe su, kuma sukar da wasu ke yi wa gwamnatin sa tamkar gyara kayan ka ne.

Sunday, December 04, 2016

BUHARI YA MAYAR WA SARKI SANUSI MARTANI KAN TATTALIN ARZIKI - BBC Hausa



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba daidai ba ne kalaman da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi cewa gwamnatinsa ta karbi N4.5tr, yana mai cewa N1.5tr ta karba.

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce, "Ina matukar mutunta mai martaba saboda shi sarkina ne; domin ni dan Kano ne. Amma akwai gyara a alkaluman da ya bayar.

Gaskiya ne gwamnati ta karbi kudi sosai daga babban bankin Najeriya, amma ba ta zarta ka'ida ba."

Shi dai Sarki Muhammadu Sanusi ya ce kudin da gwamnati ta karba daga babban bankin Najeriya sun ninka sau fiye da goma kan adadin da doka ta ba su umarni.

Sai dai Malam Garba Shehu ya kara da cewa, "Mu dauka maganar da ya fada gaskiya ce. Duk da haka gwamnati tana da kudin da ya zarta wanda ta karba a ajiye a asusun bai-daya. Kamar mutum ne mai asusun banki biyu; daya babu kudi, dayan akwai makudan kudi. Menene illar kwaso kudin daya asusun domin biyan bukatar al'umma?."

Kakakin na shugaban Najeriya ya ce ba zai yi wa Sarki Sanusi raddi kan adawar da yake yi ga kudirin gwamnati na karbi bashin $30bn, yana mai cewa ministar kudi za ta tanka masa.

A cewarsa, "A matsayi na na dan kasa zan so na sake karanta jawabinsa game da wannan batu. Amma ai za a karbo bashin ne domin yin ayyukan ci gaban kasar, cikinsu har da kafa layukan jirgin kasa da samar da hasken wutar lantarki."