Wasu mazauna garin Nguru a jihar Yobe, sun zargi hukumar ba da hasken wutar lantarki a garin PHCN da cewa da gangan suke kin barin wuta ta jima idan an kawo.
Wannan zargin na zuwa ne a Lahadin nan, wuni na uku da aka shiga cikin wadatacciyar wutar lantarki a garin da aka sake ta tun ranar Juma'a.
Wasu da wannan Dandali ya zanta da su a Nguru sun bayyana cewa, hukumar ta PHCN ta bar wutar ne a garin don kawai jin dadin wani mutum guda daya.
Suka ce a baya hukumar ta PHCN ta sha yaudararsu da cewa matsaloli ne na rashin ingantattun kayan aiki, su suka sa wutar take kin zama idan an kawo.
Malam Abubakar Sadik Bello, wani mazaunin Nguru ne dake amfani da wutar lantarki, ya ce yanzu dai ta tabbata karya ce a sake ce da mu wai rashin ingantaccen kayan aiki ne ke sa wa ba ma jimawa da wuta.
Ya kara da cewa a baya filashin suke yi mana, yanzun kuma da sun dauke da sun dawo da ita, kuma idan suka dawo da ita sai ta dade.
"kowa ya sani buki da ake a gidan Alh. Balarabe Abdullahi Nguru, shi ne ya sa aka bar wuta a gari". A cewarsa.
Shi ma dai wani mai cajin waya a Nguru Hasan Muahammad cewa ya yi, an sako wutar ce kawai saboda bikin gidan Balarabe Dj.
Kazalaka mutanen Sun kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a lamarin samar da wutar lantarki a garin da su dubi lamarin domin gano mecece matsalar da ake ta cewa ita ta hana zaman wuta.
To ko ma dai yaya ne? Wannan Dandali ya yi kokarin jin ta bakin jami'an hukumar ta PHCN domin jin martaninsu akan wannan zargi, to amma sai dai hakar Dandalin ba ta cimma ruwa ba.
Idan ba a manta ba dai, Alhajin dan kasuwa Balarabe Abdullahi Nguru ko Balarabe Dj, shi ne ya yi aikin sabunta wutar lantarki da aka kammala kwannan a daga Kano - Nguru, wadda wasu ke ganin gara jiya da yau ta fuskar tsayuwar wuta. Yayin da wasu kuma ke ganin aikin ya yi nasara.
Samun tsayayyiyar wutar lantarki a Nguru na wuni ukun da suka zo daidai da lokutan da ake shagulgulan biki a gidan hamshakin dan kasuwa Balarabe Dj dai, ya jefa shakku a zukatan wasu mazauna garin game da sahihancin zantuttukan hukumar PHCN na rashin tsayuwar wuta a garin Nguru.
Yanzun dai kallo ya koma sama, inda mutane suka zuba ido don ganin shin ko da gaske ne wutar za ta dore? Ko kuma dai hukumar ta PHCN za ta gaskata wannan zargi.

No comments:
Post a Comment