A Najeriya, masu sharhi sun fara tsokaci kan sukar da fadar shugaban kasar ke fuskanta daga wasu muhimman mutane a kasar, wadanda a baya suka kasance cikin masu goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.
Suka na baya-bayan na dai ya fito ne daga Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II wanda ya soki manufofin gwamnati na tattalin arziki.
A baya ma wasu rahotanni sun ambato tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo yana nuna takaicinsa a kan yadda al'amura ke tafiya a kasar.
Dr. Abubakar Kari malami ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja, ya ce baya ga wasu masu fada aji da ke sukar gwamnati, akwai talakawa da dama dake korafi kan yadda gwamnati ke tafiya.
Ya kara da cewa talakawa sun zabi Muhammadu Buhari ne domin ya magance matsalolin da suka addabe su, kuma sukar da wasu ke yi wa gwamnatin sa tamkar gyara kayan ka ne.

No comments:
Post a Comment