Friday, October 13, 2017

Za mu ba wa gwamnati kuri'unmu babu hamayya idan ta cika mana alkawarin dawo da zirga-zirgar mashina a jihar Yobe — Wasu mazauna jihar


Mutane da dama ne a jihar Yobe ke ci gaba da yin kiraye-kiraye ga gwamnati da ta yi wa Allah ta cika musu alkawarin dawo da sufurin mashina a fadin jihar wanda ta dauka kusan shekaru uku (3) da suka gabata.

Wannan tunatarwa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da yin ikirarin samun zaman lafiya, tare da bayyana nasarar fatattakar mayakan Boko Haram.

Mutanen sun kuma sha alwashin sadaukar da kansu ga gwamnatin a ranar zabe muddun gwamnatin ta cika wannan alkawari da ta dauka.

Wani Magidanci a garin Nguru Malam Musa Kalla ya fada a zantawarsa da wannan Dandali ranar Laraba cewa, akwai bukatar gwamnati ta dawo da zirga-zirgar mashina ko da kuwa ta mutum  dai-dai ce duba da yadda ake kara samun kyautatuwar zaman lafiya da kuma yadda ake fama da matsin rayuwa.

Malam Kalla ya ce dawo da zirga-zirgar mashinan zata taimaka wajen bunkasa fannin noma da fannin ma'aikatun gwamnati, tare da rage zaman kashe wando da dai sauransu.

Tun da farko a zantawarsa da wannan Dandali, wani Malami da ya ce a boye sunansa  ya yaba wa gwamnatin ne game da namijin kokarin da take na inganta aiki da kuma ma'aikata, da ma kokarinta na sauya fasalin jihar baki daya.

To sai dai kuma Malamin ya koka akan irin makudan kudaden da ya ce suna batarwa domin zuwa wuraren ayyukansu masu nisa sakamakon rashin sauwakakken abin hawa.

A don haka ne ma sai ya yi kira ga gwamnatin da ta taimaka musu ta hanyar dawo da sufirin mashina ko da na mutum daya ne kamar yadda ta alkawarta a baya.

Ya ci gaba da cewa hakan zai taimaka musu wajen sauke nauyin da aka dora musu da gaskiya ba tare da yin lalaci ba.

"A shekarun baya da suka shude mu ma ba za mu amince da dawo da mashinan ba, duba da yadda a lokacin babu wanzazzen zaman lafiya, amma yanzu Alhamdulillah zaman lafiya ya samu". In ji Malamin.

Idan ba a manta ba, a gabanin zaben 2015, gwamnatin jihar Yobe ta fada ta bakin kakakin gwamnan jihar Malam Abdullahi Begu a wata hira da BBC Hausa cewa, gwamnatin ba da dadewa ba zata dawo da zirga- zirgar mashina na mutum dai-dai a fadin jihar, almarin da har yanzu shiru kamar an shuka dusa.

Friday, September 22, 2017

KUNGIYAR ‘YAN KABILAR IGBO TA NAJERIYA TA BUKACI ‘YAN KANO SU ZAUNA LAFIYA DA ‘YAN KABILAR TA IGBO



Kungiyar Ohaneze Indigbo tayi kira ga al’ummar Najeriya da su yi kokarin magance bambance-bambancen da ke tsakanin su, ta hanyar tattaunawa da juna, don tabbatar da Najeriya ta zama kasa daya dunkulalliya.

Shugaban kungiyar na kasa Chief John Nwodo ne yayi wannan kiran lokacin da ya jagoranci tawagar kungiyar, tare da wasu wakilan kabilar Ogbo zuwa fadar gwamnatin jihar Kano, a wani bangare na mika sakon zaman lafiya a jihohin Arewa.

Mista John Nwodo lokacin da yake jawabi ga mukaddashin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana cewa jihar Kano tana da al’ada na karbar baki ko daga ina suke hannu bibbiyu.

A cewar sa al’ummar kasar nan na kokarin manta tashin hankalin da ya faru a shekarar 1966, amma a yanzu wasu dai-dai kun mutane na kokarin tayar da hankalin al’umma.

Gidan Rediyo Freedom da ke Kanon ya rawaito cewa Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo na kasar ya lura da cewa akwai al’ummar kabilar Igbo da suka kai kimanin miliyan daya da dubu dari shida da ke zama a jihar Kano, tare da godewa al’ummar Kano bisa karamcin da suka bawa ‘yan kabilar ta Igbo.

Da yake jawabi, mukaddashin Gwamnan jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar ya shaidawa kungiyar ta Ohaneze Indigo cewa abinda yake damun ‘yan Arewa, shine rashin tsawatarwa matasan su da shugabannin kabilar Igbon suka gaza aiwatarwa, lokacin da ake ce-ce-kucen raba Najeriya.

Thursday, September 21, 2017

KUNGIYAR KWADAGO TA BAYYANA SUNAYEN JIHOHI 10 DA SUKA KI BIYAN ALBASHI GA MA’AIKATANTA



Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana sunayen jihohi goma wadanda ta ce sune kan gaba cikin jihohin da suka ki biyan ma’aikata bashin albashi da suke binsu duk kuwa da karbar makudan kudade da aka dawo musu dashi daga kungiyar bada lamuni ta Paris Club.

Kungiyar ta NLC kamar yadda Rediyo Freedom ya habarto ta kuma ce jihohin sun ki fitowa karara su bayyana yawan kudaden ceto tattalin arzikin jihohi da gwamnatin tarayya ta basu.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa Ayuba Wabba ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

Ya ce cikin jihohi Goman akwai shida wadanda lamarin su ya fi muni, yana mai buga misali da jihar Imo wanda ya ce har I zuwa yanzu ma’aikatan jihar suna karbar albashi ne kaso-kaso haka kuma jihar ta yi kememe ta ki bayyana adadin kudaden da ta karba daga kungiyar bada lamuni ta Paris Club da kudaden ceto tattalin arzikin jihohi da ta karba daga gwamnatin tarayya.

Ayuba Wabba ya kuma bayyana jihohin Bayelsa da Ondo da Ekiti da Benue da kuma Kogi da Osun da Ebonyi da Zamfara da kuma Abia a matsayin wadanda lamarin ya yi munin gaske.

Sunday, September 17, 2017

SARKIN KANO YA YI KIRA GA MATASA DA SU GUJI YIN AIKI DA JITA-JITA



Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya kirayi al’ummar arewacin Najeriya musamman matasa da su guji yin aiki da jita-jita da kaucewa amincewa da irin sakonnin da ake aikewa ta kafafen sadarwa na zamani wanda ka iya kaiwa ga harzuka hankulan jama’a.

Sarkin na Kano ya yi wannan jan hankali ne a ranar juma’ar da ta gabata lokacin da yake gudanar da hudubar sallar juma’a.

Malam Muhammadu Sanusi II ya ce ba ya kamata ga musulmi na kwarai daukar fansa akan wanda bai aikata masa laifin komi ba, kuma dukkanin kabilun da ke zaune a jihar Kano suna zaman amana ne, sannan addinin musulunci ya harmata a cutar dasu matukar basu tankawa kowa ba.

Haka kuma sarkin ya bukaci daukacin kabilun da suke zaune a nan birnin kano da su zauna lafiya kuma kada su shigar da kawunansu cikin rigima, inda ya ce yin hakan zai haifar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar nan.

A karshe mai martaba sarkin ya bukaci limamai da sauran masu fada a ji a jihar Kano su ci-gaba da jan hankalin matasa a arewacin kasar su zauna lafiya da wadanda suke tare dasu domin kare mutuncin su da martabar addinin musulunci.

Saturday, September 16, 2017

GWAMNONIN JIHOHIN KUDU MASO GABASHIN NAJERIYA SUN YI TUR DA KUNGIYAR FAFUTUKAR KAFA KASAR BIAFRA


Daukacin gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun yi tur tare da haramta irin ayyukkan da kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB ke yi a yankin kudancin kasar.

Shugaban kungiyar Gwamnonin kuma gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ne ya sanar da hakan bayan kammala wata ganawar sirri da gwamnoni suka yi da shugabanin al’ummar kabilar Igbo da sauran masu ruwa da tsaki a fadar gwamnati da ke Enugu.

Gidan Rediyon Freedom da ke Kano ya rawaito cewa Gwamnonin sun kuma yi kira ga shugabanin kunigiyar da saura dukkanin wasu fusatattun kungiyoyo a yankin da su ayyana bukatunsu su kuma aike dasu zuwa kwamitin gwamnoni na zauren majalisar dokokin kasar nan, da kuma kungiyar Al’ummar Igbo ta Ohaneze, da zauren majalisar kasar nan karkashin shugan kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin kasar nan.

Haka kuma gwamnonin sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye sojojin da aka jibge a yankin inda suka bukaci a bar yan sanda da su ci gaba da ayyukan kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Gwamnoni dai da suka kunshi jahohi biyar sun tsai da wannan matsaya ne a wata ganawar sirri na awanni biyar da suka gudanar a fadar gwamnatin jihar Enugu wanda ya samu halartar mataimakin shugaban majalisar dattijawa Ike Ekweremadu, da shugaban kunigyar alummar Igbo ta Ohanaeze John Nwodo da kuma babban kwamandan sojin kasar nan mai lura da bataliya ta 83 laftan janar Adamu Abubakar.

Wednesday, September 13, 2017

GWAMNATIN SAUDIYYA TA YANKEWA WANI MAHAJJACI DAN JIHAR SOKOTO WATANNIN UKU A GIDAN YARI


Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zaman ta a kasar Saudiyya ta yanke wa wani mahajjaci Mallam Mamman Kwa-Kwazo hukuncin zaman Gidan kaso har na tsawon watanni uku.

Malam Mamman wanda dan asalin karamar hukumar Goronyo ne da ke jihar Sokoto, gwamnatin kasar ta same shi da lafin yin karya da mallakar wata jakar kudi da aka tsinta wadda kuma ba tashi ba ce.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin sakataren karamar hukumar Goronyo Lawal 'Yar-Tsakuwa, cewa ya yi, mahajjacin ya tsinci jakar kudin ne a harabar masallacin a ranar juma’a da ta gabata.

Rahotannin sun ce Mallam Mamman Kwa-kwazo tun da fari yaki amincewa ya bayar da jakar kudin ga mamallakinta, wanda hakan ne ya sanya aka garzaya da shi ga jami’an tsaro.

A cewar Sakataren ba a san inda bakon Gidan yarin ya fito ba, sai daga baya ne aka mika shi sansanin mahajjatan jihar Sokoton, bayan an tabbatar da cewa daga karamar hukumar da ta fito daga yankin yake, yanzu haka dai gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatar da Mamman Kwa-kwazo shiga kasar har na tsawon watanni biyar.

Thursday, September 07, 2017

AN BUKACI GWAMNATIN JIHAR YOBE DA TA SAMAR DA KANANAN TASHOSHIN FM A SHIYYOYI 3 NA JIHAR



An yi kira ga gwamnatin jihar Yobe da ta kafa karamar tashar rediyo mai watsa shirye-shirye ta zangon FM a kowace shiyya cikin shiyyoyi uku na jihar.

Wani ma'abocin sauraren radiyo Malam Ibrahim Muhd shi ya yi wannan kiran yayin zantawarsa da wannan Dandali ranar Alhamis a garin Nguru.

Malam Ibrahim Muhammad wanda ya shafe shekaru sama da talatin yana sauraren rediyo, ya ce akwai bukatar gwamnati ta wadatar da jihar da kafofin sadarwa musamman ma gidajen rediyo.

Ya ce fa'idar kafa irin wadannan tashoshin a bayyane take duba da yadda al'umomi a wannan zamani suka raja'a wajen sauraran rediyo.

Ya kara da cewa tashoshin za su taimaka wajen sauraren Rediyon jiha wanda yanzu haka ke yi wa wasu garuruwan jihar wuyar kamawa musamman garuruwan arewacin jihar.
 
A don haka sai ya bukaci gwamnatin da ta kafa rediyon shiyya (zonal Radio) a shiyyoyi ukun da suka hada da Gabaci, da Kudanci da kuma Arewacin Yobe, ta yadda sadarwa za ta saukaka a shiyyoyin da ma jihar baki daya.

Yana mai kwatanta rediyoyin a matsayin wata hanya da gwamnati da alumomi za su iya cin gajiyarsu ta fuskoki daban-daban a fadin jihar baki daya.

Saturday, September 02, 2017

NCC TA GARGADI ‘YAN NAJERIYA KAN AMFANI DA WAYOYIN JABU



Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, ta gargadi ‘yan Najeriya game da yin amfani da wayoyin salula na jabu, tare da cewar yawan amfani da su na daya daga cikin abin da ke jawo wasu nau’ika na cutar daji wato Cancer.

Wani jami’in hukumar Kunle Olorundare ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani tare da masu ruwa da tsaki, wanda hukumar ta NCC da ke shiyyar Ibadan ta shirya.

Gidan Rediyon Freedom da ke Kano ya ambato Mista Olorundare yana cewa, ya lura da cewa wayoyin salula na jabu sun samu karbuwa a fadin kasar nan, kuma yin amfani da su wata babbar barazana ce ga rayuwar al’umma.

Ya kara da cewa ire-iren wadannan wayoyin na daya daga cikin abinda ke sabbaba matasalar ayyukan sadarwa, inda yace hukumar ta NCC zata dauki mataki kan masu dillancin wayoyin na jabu.

Olorundareya kuma bukaci masu dillancin wayoyin nasalula a fadin kasar nan da su tabbatar da cewa hukumar ta amince da ingancin wayoyin da suke siya daga hannun abokan huldar su.

Sunday, August 27, 2017

ANWARUL ISLAM NGURU: Bikin yayen dalibai karo na IV



Makarantar sakandaren Anwarul Islam Nguru ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na IV tun bayan kafuwar makarantar  a matsayin cikakkiyar Sakandare a shekara ta 2007.

Bikin da aka gudanar  a safiyar Lahadin nan a harabar makarantar da ke unguwar Bulabulin, an shafe awoyi ana gabatar da shirye–shirye cikinsa.

An gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin kafin daga bisani a rarraba shahada da kyaututtuka.

A jawabinsa na bankwana da daliban, shugaban Makarantar Malam Muhammad Kabir Ali, ya ja hankulan daliban ne da su zama wakilai nagari a duk inda suka sami kansu a rayuwa.

Malam Kabir Ali ya kuma jinjinawa iyayen yara da malamai dangane da irin hobbasar da suke nunawa wajen ganin sun daga martabar ilimin yara matuka.

A na sa jawabin shugaban kwamitin Makarantar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Izala na jihar Yobe Alh. Bala Salihu Bakabe, tarihin kafuwar makarantar ya tabo.

Yana mai nuni akan irin matsalolin da makarantar take fuskanta ta bangarori daban-daban, musamman ta bangaren kayan aiki.

A don haka sai ya bukaci iyaye da sauran jama'a da su taimaka wajen ganin an wadatar da makarantar da kayan gwajin kimiyya da kuma maganadisun yanar gizo, ta yadda Makarantar za ta kasance kan gwadabe na zamani.

Da yake magana a wurin taron, shugaban karamar hukumar Nguru Alh. Ali Maidami wanda shugaban Kansiloli Hon. Litiya ya wakilta, ya sha alwashin taimakawa makarantar da dukkanin abin da bai fi karfinsu ba.

Hon. Litiya ya kuma gabatar da gudummowar kudi kimanin Naira 30,000 ga asusun makarantar a wani mataki na tallafawa wannan makaranta.

Kimanin dalibai 60 ne makarantar ta yaye daga sassa daban-daban din da suka hada da sashen haddar Alqur'ani mai girma, da na bangaren Higher Islamic da kuma na bangaren kimiyya.

Bikin da aka fara shi cikin yanayi na lullumi kafin daga bisani rana ta take, ya sami halartar jama'a da dama daga sassa daban-daban na Nguru.

Thursday, July 27, 2017

G.H.I.C NGURU: Bikin yaye dalibai karo na 22


Makarantar Higher Islamic College Nguru, ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na 22 tun bayan kafa makarantar a shekarar 1991.

Bikin da aka gudanar a safiyar Alhamis din nan a harabar makarantar dake hanyar Kano a garin Nguru, an shafe awoyi ana gudanar da shirye-shirye cikinsa.

An gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin kafin daga bisani a rarraba shahada da kyaututtuka.

A jawabinsa na ban kwana da daliban, shugaban makarantar Malam Usman Abdulmumin, ya ja hankulan daliban ne da su zama abin misali a duk inda suka tsinci kansu a rayuwa.

Yana mai shawartar su da su himmatu wajen neman ilimi domin kada su zauna kallon ruwa har kwado ya musu kafa.

Kazalika Malam Nunu, ya godewa daliban game da juriyar da suka nuna a lokacin da suke dalibai a wannan makaranta.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Malam Muhammad Sani Badamasi, wanda ke zama shugaban taron, ya godewa mahalarta taron da suka zo daga mabambantan wurare domin taya 'yan uwa da abokan arziki murnar kammala karatunsu a wannan Makaranta.

Malam Sani Badamasi, ya kuma godewa malamai da daukacin daliban da suka sami halartar wannan biki.

Kimanin dalibai sama da 250 ne makarantar ta yaye daga bangarori daban-daban da suka kunshi daliban bangaren haddar Alkur'ani mai girma, da na bangaren Higher Islamic, da kuma na bangaren Kimiyya.

Bikin da aka gunadar cikin yanayi na hadari da ruwan sama, ya sami halarta jama'a da dama daga ciki da wajen makaranta.

Wednesday, July 12, 2017

SULTAN BELLO KADUNA: Tafsirin Ramadanan bana ya bar baya da kura

Takaddama tsakanin Dr. A. Gumi da wasu Malaman Izala


Malaman Izala da dama ne a arewacin kasar nan, suka fara mayar da martani kan wasu kalamai da mai gabatar da Tafsiri a masallacin Sultan Bello Kaduna Dr. Ahmad Mahmud Gumi ya yi a tafsirinsa na watan Ramadanan da ya wuce.

Dr. Ahmad Mahmud Gumi da ga marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya yi wasu kalamai ne da suka tunzura wasu malaman na Izala har suka fara mayar da martani.

Malamai irin su Dr. Mansoor Sokoto, da Sheikh Ali Isa Pantami, da Malam Musa Yusuf  Asadus-sunnah duk sun mayar da martani kan kalaman na Ahmad Gumi.

Batutuwan da suka janyo wannan takaddama su ne batun dawowar Annabi Isa (A.S), da Dr. Gumi ya musanta, da batun kiran wasu Hadisai da ya yi da sunan Hadisan Bola.

Sai kuma batun Hadisin Sittu Shawwal da Daktan ya ce bai inganta ba, da butun musanta shigar aljani jikin bil Adama.

Sauran batutuwan sun hada da batun raunata Nasiruddeen Albany, da kuma batun Sahabi Mu'azu dan Jabal da Dr. Gumin ya ce shi ba Faqihi ba ne bisa dalilansa da ya kawo.

Malaman a martaninsu sun soki lamirin Dr. Ahmad Gumi, inda suka bayyana akidunsa da cewa akidu ne irin na Mu'tazilawa.

Suna masu kwatanta shi da cewa albasa ba ta yi halin ruwa ba.

Kazalika Malaman sun kuma zargi shi da cewa yana kokarin raba kan al'umar Musulmai, zargin da Daktan ya sha musantawa.

Yana mai cewa duk mai shakka, ko tantama kan abubuwan da ya fadi, to da kamata ya yi ya same shi su zauna a tattauna a yi zube ban kwaryata.

" Hakan ya fi alheri da ya je gefe ya aibanta ni". A cewar Ahmad Gumi.

Dr. Ahmad Mahmud Gumi mai kira da a yi riko da Mazhaba, shi ne ya gaji jujerar mahaifinsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a Sultan Bello da ke Kaduna.

Thursday, July 06, 2017

MUNA JIN DADIN WUTAR DA MUKE SAMU 'YAN KWANAKIN NAN — Inji wasu mazauna Nguru.



Mutane da dama ne a garin Nguru ke ci gaba da nuna jin dadinsu, dangane da tsayawar wutar lantarkin da aka samu a garin kwanannan.

Tsayuwar wutar da aka fara samu tun a karshen makon jiya, an kwatanta ta da cewa rabon da a sami irinta a garin an shafe shekaru.

Wani da wannan Dandali ya zanta da shi ranar Alhamis a Nguru Malam Ibrahim Mustapha, ya yi fatan dorewar wutar ta yadda ba za a sake dauke ta a garin kwata-kwata ba.

Ba a san dai ko menene hakikanin dalilin tsayuwar wutar a garin na 'yan kwanakin nan ba, domin kokarin jin ta Kamfanin da wannan Dandali ya cutura.

A baya dai wasu al'umomi a Nguru, sun sha dora alhakin rashin samun wutar lantarkin a kan kamfanin da ke ba wa garin  wuta daga shiyyar Kano, da cewa shi ne ke hana su wutar  da gangan.

Thursday, June 22, 2017

TSAKANINMU DA GWAMNA SAI GODIYA — In ji wasu ma'aikatan Yobe


Mai girma Gwamnan jihar Yobe Alh. Ibrahim Gaidam

Wasu ma'aikata a jihar Yobe na ci gaba da nuna godiyarsu ga gwamnatin jihar sakamakon albashinsu da ta biya su tun daga yanzun domin yin hidimar Sallah.

A tattaunawarsu da wannan Dandali jim kadan bayan sun sami albashinsu a garin Nguru, ma'aikatan suka ce hakan ya kara musu karfin gwuiwar da su ma za su yi bushasha sosai a bukukuwan Sallar bana.

Tun a jiya Laraba ne dai ma'aikatan suka fara ganin sakon biyansu hakkokinsu, inda saura suka karbi nasu sakon a yau Alhamis.

Wani ma'aikaci a Nguru da ya ce a boye sunansa ya ce, hakan abin a yaba ne kuma yana godewa Gwamna Ibrahim Gaidam.

Ya kara da cewa, abinka da dan albashi kullum yana cikin taraddadin ko ta wacce hanya ce zai warware matsaloli, musamman ma a irin wadannan lokuta da ake batar da kudade wajen yin hidimomi.

Ya ce, amma da zuwan wannan albashi to ka gani ai hakan zai taimaka matuka.

Kazalika wani ma'aikacin da shi ma ya ce a boye sunansa ya bayyana godiyarsa ce ga gwamna Ibrahim Geidam.

Yana mai yin kira ga gwamnan da ya duba batun yiwuwar biyan kudaden hutun nan da ake ta yayata labarinsu a 'yan lokutan baya.

Har wa yau ya kuma yi kira ga gwamnatocin kananan hukumomi da su yi koyi da gwamnatin jihar wajen biyan ma'aikatansu hakkokinsu kafin ranar Sallah.

Da ma dai tun da farko, gwamnatin jihar ta fada ta bakin kakakinta Alh Abdullahi Begu a wani bayani da Abubakar Ibn Usman ya nakalto a shafinsa na facebook a safiyar Laraba 21/06/017, cewa tini mai aikatar kudi ta jihar har ta aika da kudaden maikatan zuwa bankuna domin bayarwa

Friday, June 09, 2017

AN BUƘACI MUSULMAI DA SU RIƘA TAIMAKON JUNA CIKIN RAMADANA


An yi kira ga al'umar Musulmai da su dage wajen taimakon juna ciki watan Ramadana domin cin ribar rayuwa.

Babban Limamin masallacin Juma'a na ƙungiyar Jama'atu Izalatul bid'ah wa iƙamatussunna Al-sheikh Muhd Baba Nguru ne ya buƙaci hakan a huɗubarsa ta Sallar Juma'a yau a garin Nguru.

Al-sheikh Baba Nguru ya ce taimaka wa talakawa, da miskinai, da marayu, da zawarawa da abin da za su ci, na sa Allah (swt) ya yaye wa al'uma baƙin ciki da bala'in ƙuncin rayuwa.

Kazalika Sheikh Muhd Baba ya kawo ayoyi daga cikin Alƙur'ani mai girma da hadisan manzon Allah (saw) da suke nuni game da falala da alherin ciyar da mai yin Azumi.

Daga nan sai Shehun Malamin ya zaburar da musulman akan su ƙara azama wajen Sallar dare, da kuma yin Sallah tare da liman a Masallaci, da aikata dukkanin ayyukan alheri tare da ƙauracewa ayyukan assha.

Sheikh Muhd Baba, daga ƙarshe ya yi addu'oin fatan alheri da addu'ar samun zaman lafiya da rangwamen ƙuncin rayuwa da ya addabi al'umar ƙasa baki ɗaya.