Mutane da dama ne a garin Nguru ke ci gaba da nuna jin dadinsu, dangane da tsayawar wutar lantarkin da aka samu a garin kwanannan.
Tsayuwar wutar da aka fara samu tun a karshen makon jiya, an kwatanta ta da cewa rabon da a sami irinta a garin an shafe shekaru.
Wani da wannan Dandali ya zanta da shi ranar Alhamis a Nguru Malam Ibrahim Mustapha, ya yi fatan dorewar wutar ta yadda ba za a sake dauke ta a garin kwata-kwata ba.
Ba a san dai ko menene hakikanin dalilin tsayuwar wutar a garin na 'yan kwanakin nan ba, domin kokarin jin ta Kamfanin da wannan Dandali ya cutura.
A baya dai wasu al'umomi a Nguru, sun sha dora alhakin rashin samun wutar lantarkin a kan kamfanin da ke ba wa garin wuta daga shiyyar Kano, da cewa shi ne ke hana su wutar da gangan.

No comments:
Post a Comment