Wednesday, July 12, 2017

SULTAN BELLO KADUNA: Tafsirin Ramadanan bana ya bar baya da kura

Takaddama tsakanin Dr. A. Gumi da wasu Malaman Izala


Malaman Izala da dama ne a arewacin kasar nan, suka fara mayar da martani kan wasu kalamai da mai gabatar da Tafsiri a masallacin Sultan Bello Kaduna Dr. Ahmad Mahmud Gumi ya yi a tafsirinsa na watan Ramadanan da ya wuce.

Dr. Ahmad Mahmud Gumi da ga marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya yi wasu kalamai ne da suka tunzura wasu malaman na Izala har suka fara mayar da martani.

Malamai irin su Dr. Mansoor Sokoto, da Sheikh Ali Isa Pantami, da Malam Musa Yusuf  Asadus-sunnah duk sun mayar da martani kan kalaman na Ahmad Gumi.

Batutuwan da suka janyo wannan takaddama su ne batun dawowar Annabi Isa (A.S), da Dr. Gumi ya musanta, da batun kiran wasu Hadisai da ya yi da sunan Hadisan Bola.

Sai kuma batun Hadisin Sittu Shawwal da Daktan ya ce bai inganta ba, da butun musanta shigar aljani jikin bil Adama.

Sauran batutuwan sun hada da batun raunata Nasiruddeen Albany, da kuma batun Sahabi Mu'azu dan Jabal da Dr. Gumin ya ce shi ba Faqihi ba ne bisa dalilansa da ya kawo.

Malaman a martaninsu sun soki lamirin Dr. Ahmad Gumi, inda suka bayyana akidunsa da cewa akidu ne irin na Mu'tazilawa.

Suna masu kwatanta shi da cewa albasa ba ta yi halin ruwa ba.

Kazalika Malaman sun kuma zargi shi da cewa yana kokarin raba kan al'umar Musulmai, zargin da Daktan ya sha musantawa.

Yana mai cewa duk mai shakka, ko tantama kan abubuwan da ya fadi, to da kamata ya yi ya same shi su zauna a tattauna a yi zube ban kwaryata.

" Hakan ya fi alheri da ya je gefe ya aibanta ni". A cewar Ahmad Gumi.

Dr. Ahmad Mahmud Gumi mai kira da a yi riko da Mazhaba, shi ne ya gaji jujerar mahaifinsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a Sultan Bello da ke Kaduna.

No comments:

Post a Comment