Thursday, July 27, 2017

G.H.I.C NGURU: Bikin yaye dalibai karo na 22


Makarantar Higher Islamic College Nguru, ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na 22 tun bayan kafa makarantar a shekarar 1991.

Bikin da aka gudanar a safiyar Alhamis din nan a harabar makarantar dake hanyar Kano a garin Nguru, an shafe awoyi ana gudanar da shirye-shirye cikinsa.

An gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin kafin daga bisani a rarraba shahada da kyaututtuka.

A jawabinsa na ban kwana da daliban, shugaban makarantar Malam Usman Abdulmumin, ya ja hankulan daliban ne da su zama abin misali a duk inda suka tsinci kansu a rayuwa.

Yana mai shawartar su da su himmatu wajen neman ilimi domin kada su zauna kallon ruwa har kwado ya musu kafa.

Kazalika Malam Nunu, ya godewa daliban game da juriyar da suka nuna a lokacin da suke dalibai a wannan makaranta.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Malam Muhammad Sani Badamasi, wanda ke zama shugaban taron, ya godewa mahalarta taron da suka zo daga mabambantan wurare domin taya 'yan uwa da abokan arziki murnar kammala karatunsu a wannan Makaranta.

Malam Sani Badamasi, ya kuma godewa malamai da daukacin daliban da suka sami halartar wannan biki.

Kimanin dalibai sama da 250 ne makarantar ta yaye daga bangarori daban-daban da suka kunshi daliban bangaren haddar Alkur'ani mai girma, da na bangaren Higher Islamic, da kuma na bangaren Kimiyya.

Bikin da aka gunadar cikin yanayi na hadari da ruwan sama, ya sami halarta jama'a da dama daga ciki da wajen makaranta.

No comments:

Post a Comment