Sunday, August 27, 2017

ANWARUL ISLAM NGURU: Bikin yayen dalibai karo na IV



Makarantar sakandaren Anwarul Islam Nguru ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na IV tun bayan kafuwar makarantar  a matsayin cikakkiyar Sakandare a shekara ta 2007.

Bikin da aka gudanar  a safiyar Lahadin nan a harabar makarantar da ke unguwar Bulabulin, an shafe awoyi ana gabatar da shirye–shirye cikinsa.

An gabatar da jawabai daban-daban a wurin bikin kafin daga bisani a rarraba shahada da kyaututtuka.

A jawabinsa na bankwana da daliban, shugaban Makarantar Malam Muhammad Kabir Ali, ya ja hankulan daliban ne da su zama wakilai nagari a duk inda suka sami kansu a rayuwa.

Malam Kabir Ali ya kuma jinjinawa iyayen yara da malamai dangane da irin hobbasar da suke nunawa wajen ganin sun daga martabar ilimin yara matuka.

A na sa jawabin shugaban kwamitin Makarantar wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Izala na jihar Yobe Alh. Bala Salihu Bakabe, tarihin kafuwar makarantar ya tabo.

Yana mai nuni akan irin matsalolin da makarantar take fuskanta ta bangarori daban-daban, musamman ta bangaren kayan aiki.

A don haka sai ya bukaci iyaye da sauran jama'a da su taimaka wajen ganin an wadatar da makarantar da kayan gwajin kimiyya da kuma maganadisun yanar gizo, ta yadda Makarantar za ta kasance kan gwadabe na zamani.

Da yake magana a wurin taron, shugaban karamar hukumar Nguru Alh. Ali Maidami wanda shugaban Kansiloli Hon. Litiya ya wakilta, ya sha alwashin taimakawa makarantar da dukkanin abin da bai fi karfinsu ba.

Hon. Litiya ya kuma gabatar da gudummowar kudi kimanin Naira 30,000 ga asusun makarantar a wani mataki na tallafawa wannan makaranta.

Kimanin dalibai 60 ne makarantar ta yaye daga sassa daban-daban din da suka hada da sashen haddar Alqur'ani mai girma, da na bangaren Higher Islamic da kuma na bangaren kimiyya.

Bikin da aka fara shi cikin yanayi na lullumi kafin daga bisani rana ta take, ya sami halartar jama'a da dama daga sassa daban-daban na Nguru.

No comments:

Post a Comment