Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, ta gargadi ‘yan Najeriya game da yin amfani da wayoyin salula na jabu, tare da cewar yawan amfani da su na daya daga cikin abin da ke jawo wasu nau’ika na cutar daji wato Cancer.
Wani jami’in hukumar Kunle Olorundare ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani tare da masu ruwa da tsaki, wanda hukumar ta NCC da ke shiyyar Ibadan ta shirya.
Gidan Rediyon Freedom da ke Kano ya ambato Mista Olorundare yana cewa, ya lura da cewa wayoyin salula na jabu sun samu karbuwa a fadin kasar nan, kuma yin amfani da su wata babbar barazana ce ga rayuwar al’umma.
Ya kara da cewa ire-iren wadannan wayoyin na daya daga cikin abinda ke sabbaba matasalar ayyukan sadarwa, inda yace hukumar ta NCC zata dauki mataki kan masu dillancin wayoyin na jabu.
Olorundareya kuma bukaci masu dillancin wayoyin nasalula a fadin kasar nan da su tabbatar da cewa hukumar ta amince da ingancin wayoyin da suke siya daga hannun abokan huldar su.

No comments:
Post a Comment