Thursday, September 07, 2017

AN BUKACI GWAMNATIN JIHAR YOBE DA TA SAMAR DA KANANAN TASHOSHIN FM A SHIYYOYI 3 NA JIHAR



An yi kira ga gwamnatin jihar Yobe da ta kafa karamar tashar rediyo mai watsa shirye-shirye ta zangon FM a kowace shiyya cikin shiyyoyi uku na jihar.

Wani ma'abocin sauraren radiyo Malam Ibrahim Muhd shi ya yi wannan kiran yayin zantawarsa da wannan Dandali ranar Alhamis a garin Nguru.

Malam Ibrahim Muhammad wanda ya shafe shekaru sama da talatin yana sauraren rediyo, ya ce akwai bukatar gwamnati ta wadatar da jihar da kafofin sadarwa musamman ma gidajen rediyo.

Ya ce fa'idar kafa irin wadannan tashoshin a bayyane take duba da yadda al'umomi a wannan zamani suka raja'a wajen sauraran rediyo.

Ya kara da cewa tashoshin za su taimaka wajen sauraren Rediyon jiha wanda yanzu haka ke yi wa wasu garuruwan jihar wuyar kamawa musamman garuruwan arewacin jihar.
 
A don haka sai ya bukaci gwamnatin da ta kafa rediyon shiyya (zonal Radio) a shiyyoyi ukun da suka hada da Gabaci, da Kudanci da kuma Arewacin Yobe, ta yadda sadarwa za ta saukaka a shiyyoyin da ma jihar baki daya.

Yana mai kwatanta rediyoyin a matsayin wata hanya da gwamnati da alumomi za su iya cin gajiyarsu ta fuskoki daban-daban a fadin jihar baki daya.

No comments:

Post a Comment