Friday, August 05, 2011

An bukaci Musulmai da su dinga taimakon juna cikin Ramadana.




An bukaci al'umar Musulmai da su zama masu taimakon junansu,musamman a kwanakin watan Azumin Ramadan don cin ribar rayuwa.

Babban limamin masallacin Juma'a na kungiyar Jama'atu Izalatul bid'a wa iqamatus sunna Al-shaikh Muhammad Khamis Ya'u Bello ne ya bukaci hakan a hudubarsa ta Sallar Juma'a yau a garin Nguru.

Shaikh Khamisu ya kara da cewa, watan Ramadana wata ne da ake bukatar duk wani Musulmi ya rubanya ibadunsa ga Allah (S.W.T), tare da yawaita karatun Alkur'ani mai girma da kauracewa ayyukan assha.

Shehun malamin har wa yau ya bukaci musulmin da su zama masu yawaita kyaututtuka, da sadaka ta hanyar taimakawa gajiyayyun cikinsu da abinci ko sutura, da kuma sauran kayayyaki irin na masarufi. A cewarsa ta haka ne 'yan uwantakar addini zata kara karfi.

Hakazalika malam Khamisu ya kawo ayoyi daga cikin Al,kur'ani mai girma, da Hadisan manzon Allah (S.A.W), inda ya tunatar wa musulman game da falalar ciyar da mai yin azumi da kyautata masa, ya ce yin hakan shi ne cin ribar rayuwa.

Al-shaikh Khamisu daga karshe, ya yi addu'ar fatan alheri, tare da addu'ar samun zaman lafiya ga mazauna garin Maidugiri ta jihar Borno da ma Najeriya baki daya.

No comments:

Post a Comment