
An bukaci matasa 'yan yi wa kasa hidima da su zama masu dogaro da kansu a duk inda suka sami kansu a rayuwa.
Shugaban hukuma mai kula da 'yan yi wa kasa hidima ta kasa,Birgediya Mahrazu Isma'ila Tsiga ne ya bukaci hakan jiya a lokacin da ya ziyarci sansanin horar da matasa 'yan yi wa kasa hidima dake karamar hukumar Girie ta jihar Adamawa.
Birgediya Tsiga,wanda shugabar hukumar mai kula da jihohin Arewa maso gabar madam Roda Kaka Kwaki ta wakilta,ya ce matasan 'yan yi wa kasa hidima wani madubi ne na al'uma,wadanda sai da su ne kasa zata ci gaba.
Madam Kwaki har wa yau ta bayyana matasan da cewa su ne kashin bayan ci gaban kowace al'uma ta da da ta yanzu. A cewarta ya zama dole ga matasan da su zama masu dogaro da kai ta hanyar yi tare da kirkirar sana'o'i,kazalika madam Kwaki ta ce hukumarsu a shirye take da ta taimaka wa irin wadannan matasa don ganin sun sami hanyar dogaro da kansu bayan sun kammala ayyukansu na hidimar kasa.
Daga karshe,madan Kwaki ta tabbatar wa matasan karin albashinsu da gwamnatin tarayya ta yi musu na N19800,maimakon N9700n da aka saba biya a baya. Sa'annan ta bukace su da zama masu hali nagari a duk inda suka sami kansu a fadin jihar ta Adamawa.
No comments:
Post a Comment