Na gina wannan Dandali ne don fadakarwa da tunatarwa, tare da yin hannunka mai sanda. Wani lokaci kuma Dandalin zai zo muku da labaran gida Najeriya, da Afirka da ma duniya baki daya.
Bai tsaya a nan ba, Dandalin har wa yau zai rika zuwa muku da tatsuniyoyi da almara da sauran labaran nishadi da nishadantarwa. Allah ya taimake mu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta sake dage zaben 'yan majalisar tarayya da za a gudanar da a gobe litinin zuwa ranar Asabar ta mako mai zuwa.