Friday, June 09, 2017

AN BUƘACI MUSULMAI DA SU RIƘA TAIMAKON JUNA CIKIN RAMADANA


An yi kira ga al'umar Musulmai da su dage wajen taimakon juna ciki watan Ramadana domin cin ribar rayuwa.

Babban Limamin masallacin Juma'a na ƙungiyar Jama'atu Izalatul bid'ah wa iƙamatussunna Al-sheikh Muhd Baba Nguru ne ya buƙaci hakan a huɗubarsa ta Sallar Juma'a yau a garin Nguru.

Al-sheikh Baba Nguru ya ce taimaka wa talakawa, da miskinai, da marayu, da zawarawa da abin da za su ci, na sa Allah (swt) ya yaye wa al'uma baƙin ciki da bala'in ƙuncin rayuwa.

Kazalika Sheikh Muhd Baba ya kawo ayoyi daga cikin Alƙur'ani mai girma da hadisan manzon Allah (saw) da suke nuni game da falala da alherin ciyar da mai yin Azumi.

Daga nan sai Shehun Malamin ya zaburar da musulman akan su ƙara azama wajen Sallar dare, da kuma yin Sallah tare da liman a Masallaci, da aikata dukkanin ayyukan alheri tare da ƙauracewa ayyukan assha.

Sheikh Muhd Baba, daga ƙarshe ya yi addu'oin fatan alheri da addu'ar samun zaman lafiya da rangwamen ƙuncin rayuwa da ya addabi al'umar ƙasa baki ɗaya.

No comments:

Post a Comment