Saturday, September 16, 2017

GWAMNONIN JIHOHIN KUDU MASO GABASHIN NAJERIYA SUN YI TUR DA KUNGIYAR FAFUTUKAR KAFA KASAR BIAFRA


Daukacin gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun yi tur tare da haramta irin ayyukkan da kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB ke yi a yankin kudancin kasar.

Shugaban kungiyar Gwamnonin kuma gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ne ya sanar da hakan bayan kammala wata ganawar sirri da gwamnoni suka yi da shugabanin al’ummar kabilar Igbo da sauran masu ruwa da tsaki a fadar gwamnati da ke Enugu.

Gidan Rediyon Freedom da ke Kano ya rawaito cewa Gwamnonin sun kuma yi kira ga shugabanin kunigiyar da saura dukkanin wasu fusatattun kungiyoyo a yankin da su ayyana bukatunsu su kuma aike dasu zuwa kwamitin gwamnoni na zauren majalisar dokokin kasar nan, da kuma kungiyar Al’ummar Igbo ta Ohaneze, da zauren majalisar kasar nan karkashin shugan kungiyar gwamnonin kudu maso gabashin kasar nan.

Haka kuma gwamnonin sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye sojojin da aka jibge a yankin inda suka bukaci a bar yan sanda da su ci gaba da ayyukan kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.

Gwamnoni dai da suka kunshi jahohi biyar sun tsai da wannan matsaya ne a wata ganawar sirri na awanni biyar da suka gudanar a fadar gwamnatin jihar Enugu wanda ya samu halartar mataimakin shugaban majalisar dattijawa Ike Ekweremadu, da shugaban kunigyar alummar Igbo ta Ohanaeze John Nwodo da kuma babban kwamandan sojin kasar nan mai lura da bataliya ta 83 laftan janar Adamu Abubakar.

No comments:

Post a Comment