Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya kirayi al’ummar arewacin Najeriya musamman matasa da su guji yin aiki da jita-jita da kaucewa amincewa da irin sakonnin da ake aikewa ta kafafen sadarwa na zamani wanda ka iya kaiwa ga harzuka hankulan jama’a.
Sarkin na Kano ya yi wannan jan hankali ne a ranar juma’ar da ta gabata lokacin da yake gudanar da hudubar sallar juma’a.
Malam Muhammadu Sanusi II ya ce ba ya kamata ga musulmi na kwarai daukar fansa akan wanda bai aikata masa laifin komi ba, kuma dukkanin kabilun da ke zaune a jihar Kano suna zaman amana ne, sannan addinin musulunci ya harmata a cutar dasu matukar basu tankawa kowa ba.
Haka kuma sarkin ya bukaci daukacin kabilun da suke zaune a nan birnin kano da su zauna lafiya kuma kada su shigar da kawunansu cikin rigima, inda ya ce yin hakan zai haifar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar nan.
A karshe mai martaba sarkin ya bukaci limamai da sauran masu fada a ji a jihar Kano su ci-gaba da jan hankalin matasa a arewacin kasar su zauna lafiya da wadanda suke tare dasu domin kare mutuncin su da martabar addinin musulunci.

No comments:
Post a Comment