Sunday, June 30, 2019

MU MUKA SA KANMU AIKIN GAYYA BA WANI NE YA SAKA MU BA

Matasa na kan aikin yashe magudanan ruwa a Bulabulin Nguru

Wasu matasa a Bulabulin Nguru da suka gudanar da aikin yashe magudanan ruwa a yau Lahadi sun musanta cewa wai saka su aka yi domin su yashe magudanan ruwa a wasu sassan unguwar.

Matasan sun karyata bayanan ne biyo bayan abin da suka kwatanta da farfaganda da wasu suke yadawa a kafafen sada zumunta kan cewa wai mahunkuntan gari ne suka umarci da a gudanar da aikin.

A zantawarsu da Wannan Dandali a yau Lahadi jim kadan bayan sun kammala aikin yau da suka somo shi ta magudanan ruwan titin Zakariya Mai malari (Layin Marigayi Haruna Pharmacy ko ko layin Abdulhamidi ko na marigayi Alh. Ari Machina), matasan suka ce za su ci gaba gobe idan Allah ya kai mu ta layin Alh. Kwalle inda suke sa ran danganawa da layin Alh. Adam mai mota.

Shugaban masu gudanar da aikin da ya bukaci a boye sunansa ya ce duk shekara sun saba gudanar da Wannan aiki, kuma rashin adalci ne a ce wasu ne suka saka a a yi aikin a yanzu.

Ya ce bai sani ba ko a wani wuri, amma su dai domin radin kansu suka gudanar da aikin.

Daya daga cikin masu aikin kuma na hannun damar Hon. Lawan Sani, Musa Mati wanda aka fi sani da Musa kafar yawo ya shaida wa Wannan Dandali cewa aikin na ganin damarsu ne bai wai umarni ne na mahunkuntan gari ba.

Ya ce babu azzalimi kamar wanda ya alakanta aikinsu da umarnin mahunkunta.

Tunda farko Hon. Lawan Sani dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya a jiya Asabar ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook inda yake gayyatar magoya bayansa da su fito a gobe Litinin da misalin 6:00 na safe domin sanya tubalin aikin yashe magudanan ruwan da za a somo daga arewacin garin Nguru.

No comments:

Post a Comment