Saturday, July 06, 2019

Ana ci gaba da aikin Hon. Lawan Sani na feshin maganin sauro gida-gida a garin Nguru.


Tun a ranar Larabar 3 ga watan Yulin nan ne Hon. Lawan Sani Inuwa dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya a majalisar jiha ya kaddamar da Shirin YAKI DA ZAZZABIN CIZON SAURO da aka fara da feshin magunguna a gidajen daukacin Unguwannin cikin gari guda hudu(4).

An kaddamar da Shirin ne kwanaki biyu kacal da aka gano dan majalisar da jama'arsa suna yashe wasu magudanan ruwa.

Jama'a na ci gaba da nuna jin dadi da farin ciki kan aikin feshin wanda a yau Asabar aikin ya shiga kwanaki na 5.

Wakilin Wannan Dandali ya yi kicibis da wasu ma'aikatan feshin a yau Asabar a Bulabulin ya kuma tambaye su ko yaya aikin yake gudana?

Daya daga cikin Ma'aikatan Musa Mal. Mati da aka fi sani da Kafar Yawo ya tabbatar da gamsuwar jama'a kan aikin na feshin Sauro.

Kafar Yawo wanda wakilin Dandalin ya tare shi a daidai lokacin da yake fitowa daga wani gida bayan ya feshe su da maganin a Bulabulin ta 2 ya ce aiki yana gudana kuma al'uma na ci gaba da yi wa Hon. Lawan addu'o'i.

Ya ce tunda suka somo aikin a ranar Laraba ba su fiskanci wata matsala ba, hasali ma sai tarbar arziki da suke samu gida-gida.

Kazalika Wannan Dandali ya sake kicibis da wasu ma'aikatan feshin guda biyu a a yayin da suke aikin na feshin a unguwar ta Bulabulin jim kadan bayan ya zanta da Kafar Yawo a yau Asabar.

Ma'aikatan biyu Rabi'u Muhammad da Lawan Musa su ma sun tabbatar da cewa aikin ya sami karbuwa a wurin jama'ar gari.

Suka ce mutane na tarbar su hannu biyu-biyu inda har wasu kan yi musu alherin ruwan Sanyi.


Shi ma dai shugaban ma'aikatan a unguwar Bulabulin  Sabo Pillars ya tabbatar da aikin na tafiya daidai.

Yana mai cewa tini har sun kammala da yankin Bulabulin ta 1 tun a ranar Jama'a, inda suke sa ran kammalawa da Bulabulin ta 2 da Bulabulin ta 3 daga Asabar din yau zuwa ranar Litinin din 8 ga watan Yulin 2019.
Wani sashen gari Nguru

Pillars ya ce Ma'aikatansu shida-shida aka tura sauran Unguwanni 3 da suka hada da Hausari, Tsohon Nguru da Sabon garin Kanuri a halin yanzu na ci gaba da aikin feshin safe da rana.

No comments:

Post a Comment