Saturday, August 08, 2020

Makarantu sun koma a jihar Yobe, malamai na ci gaba da tsara jadawalin duba masu daukar jarabawa

Malamai da daliban aji 3 na babbar Sakandaren kwana a jihar Yobe sun koma makarantunsu a yau Asabar.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta umarci makarantun Sakandare a jihar da su koma a ranakun 8 da kuma 11 ga watan Agusta 2020 domin tunkarar jarabawar WAEC ga daliban azuzuwan karshe.

A karamar hukumar Nguru a mafiya yawan makarantun daliban ba su koma ba tukunna.

Duk kuwa da cewa sanarwar da ma'aikatar ilimin jihar ta fitar a ranar Laraba ta nuna cewa makarantu masu zaman kansu za su koma ne a ranar Talatar 11 ga watan Agusta.

To sai dai an sami wasu makarantun Sakandare masu zaman kansu na Islamiyoyi a garin da suka koma tun a yau Asabar.

Wakilin wannan Dandali a yau Asabar ya ziyarci Makarantar Higher Islam ya kuma ba da labarin cewa dalibai kadan ne suka koma a yau Asabar, galibin wadanda suka koma su ne ma'aikata.

Malam Dahiru Usman Alfullaty, daya ne daga cikin Malaman da suka koma a yau Asabar, a zantawarsa da wannan Dandali ya bayyana cewa akwai tsirarun daliban da suka koma, amma galibinsu suna cikin kayan gida.

Ya kara da cewa a halin yanzu malamai sun dukufa wajen tsara jadawalin ajin karatu na musamman ga daliban da na masu dubu su a yayin da suke daukar jarabawarsu ta karshe da za fara mako mai zuwa.

Idan ba a manta ba Gwamnatin tarayya a kwanannan ta umarci daliban aji 3 na makarantun Sakandare a fadin kasa da su koma makarantunsu a ranar 4 ga watan Agusta, bayan sun shafe watanni 5 a gida, inda a jihar Yobe sai a Asabar din nan ce a ka bude makarantun.

No comments:

Post a Comment