Kungiyar malaman jami`o`i ta kasa ASUU, ta yi barazanar shiga yajin
aikin gargadi daga ranar 2 ga watan Oktoba mai zuwa.
A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar a Litinin din nan mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na reshen jami`ar
Abuja Mr. Ben Ugheoke, kungiyar ta ce gwamnatin tarayya ta gaza wajen sake komawa
teburi tattaunawa da shgabannin kungiyar domin ganin an aiwatar da alkawuran da
gwamnatin ta dauka a 2009 na inganta jami`o`in kasar.
Jaridar Premium Times ta nakalto jawabin yana cewa, ``mun yi kokarin
ganin cewa gwamnati ta saurare mu, to amma sai muka fahimci cewa gwamnatin na
wasa ne kawai da hankulanmu, a saboda
haka ne muka kudiri aniyar shiga yajin aikin gargadi na tsawo mako guda, daga
ranar 2 ga watan Oktoban nan mai zuwa,
domin nunawa gwamnati cewan mu ba da
wasa muke ba``.
Jawabin ya ci gaba da cewa, ``za mu shiga yajin aiki na sai baba ta gani, idan har
gwamnati ta kasa yin wani abu na azo a gani bayan mun kamala yajin aikin
gargadi ``.
Idan dai za a iya tinawa, a shekara ta 2009 ne gwamnatin tarayyar
Najeriya, ta dauka wa uawar kungiyar ta ASSU wasu alkawuran inganta jami`o`in
kasar, wanda kawo yanzu a cewa ASSUn, kasha 30 bisa 100 ne na alkawuran kawai
gwamnatin ta aiwatar.

No comments:
Post a Comment