Wasu ma`aikata a garin Nguru jihar Yobe, sun koka game da matsalar rashin albashi na tsawon watanni biyu, ba tare da an biya su albashi ba.
A tattaunawar da aka yi da su a garin Nguru, ma`aikatan suka ce sun kasa fahimtar dalilin da ya sa gwamnatin jihar ke ta ja musu rai a duk lokacin da aka zo biyan albashi.
Suka ce, ga rayuwa ta tsananta, ga ba albashi, al`amarin da ya jefa da damansu cikin mayuwcin hali, inda da yawansu suka dogara da `yan uwa da abokan arziki wajen naiman taimako.
Ma`aikatan sun kuma yi kira ga gwamnati da ta yi wa Allah ta biya su albashinsu cikin makon nan domin su sami abin da za su yi hidimar Sallah mai karatowa.
A nata bangaren, gwamnatin jihar ta ce, bincike ne ake gudarwa domin samun sahihin alkaluman ma`aikatan gaskiya, wanda a cewarta, matsalar an kusa shawo kanta, kuma za a biya ma`aikatan da zarar an gama bincike.
A tsakiyar watan Yuli ne kwamitin gudanar da binciken da gwamnatin jihar Yobe ta kafa suka ziyarci wasu kananan hukumomi biyar da matsalar ta shafa, domin gudanar da aikinsu, sai dai wasu na ganin kwamitin yana tafiyar hawainiya wajen guanar da aikin nasu.

No comments:
Post a Comment