A karamar hukumar Nguru a jihar Yobe, a Asabar din nan an wayi gari da wani mummunan labarin wani hadarin jirgin ruwa da ya ritsa da wasu mahaya jirgin
ruwan fito, wadanda suka hada mazauna garin.
Bayanai sun ce hadarin ya faru ne da marecen jiya Juma'a, a sakamakon wata mahaukaciyar iska da aka yi, a daidai lokacin da suke cikin jirgin akan hanyarsu ta ruwa daga Adiyani - Nguru, lamarin da janyo kifewar jirgin nasu a cikin ruwa. mutane sama da 10 ne suka rasa rayukansu a wannan hadari.
A daya hannun kuma, muna mika sakon ta'aziya ga 'yan uwan Malama Maryam Umar, wacce ake kira mai kwale, da ita ma aka yi jana'izarta yau a unguwar Bulabulin Nguru.
Allah ya jikan su da rahama, ya sa al'janna ce makomarsu. Idan ta mu ta zo, Allah ya sa mu cika da kyau da imani, amin.

No comments:
Post a Comment