Saturday, March 19, 2011

Za a yi amfani da jiragen sama masu saukar Angulu wajen gudanar da zabe a jihar Yobe.


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar Yobe, ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryenta na samar da jiragen sama masu saukar Angulu don gudanar da ayyukan zabe a jihar Yobe.

Baturen zaben jihar Malam Sadiq Musa shi ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a Damaturu.

Malam Musa ya ce za a yi amfani da jiragen ne domin saukaka ayyukan zabe a kananan hukumomi 12 daga cikin kananan hukumomi 17 na jihar wadanda hukumar tasa kan fuskanci matsaloli daban-daban sakamakon yawaitar hamadar sahara a lokutan zabe.

Ya kara da cewa ana sa ran isowar wadannan jirage nan da karshen wannan wata.

Daga nan sai ya bukaci jam'iyyun siyasa da masarautun gargajiya, tare da shugabannin addinai, da kungiyoyi daban-daban, da su ba wa ma'aikatan hukumarsa hadin kai a lokutan babban zabe mai zuwa,don ganin an gudanar da zabe mai tsafta a dukkan fadin jihar.

No comments:

Post a Comment