Jama'a a garin Nguru jihar Yobe har ma da wasu a wajen Nguru na ci gaba da shi albarka ga dan majalisa mai wakiltar Nguru ta tsakiya a majalisar jiha Hon. Lawan Sani.
Wannan fatan alheri na zuwa ne tun bayan bayyanar wani hoto da Hon. Lawan Sani ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis a cikin ruwan sama.
A hoton an gano dan majalisar a gidajen wasu talakawa da ruwa ya mamaye a sakamakon ruwan sama kamar da bakin Kwarya da aka shafe awoyi ana tafka shi tun da asubahin ranar Alhamis a garin Nguru.
Dan majalisar da aka kwatanta aikinsa da na Sayyadina Umar(R.A) ya rubuta cewa mutanen da bala'in ya shafa za su sami tallafi daga kungiyoyin agajin gaggawa tare da gwamnatin jihar Yobe.
Hon. Lawan ya ce: "A yau da karfe shida na safe 6:00am na fita dan naga irin damuwar da al'ummar mu suka shiga ah sa nadiyar ruwan sama kuma Inshaa Allah Gomnatin Yobe zata kawo mana gudun mawa"( and other agencies for intervention). Allah Ya taimaki Al'ummar mu!!!".
Tun daga bayyanar sakon ne jama'a ta ci gaba da martani inda wasu suka ce abin da dan majalisar ya yi aiki ne irin na magabatan farko.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa dan majalisar dake wakiltar Nguru a karo na farko bayan ya kada na jam'iyyar APC mai ya shiga an kwashe ruwan da ya mamaye wadannan gidaje ba tare da ya sanar da kowa ba.
Ruwan saman na ranar Alhamis ya janyo asara mai yawa da rushewar gidaje al'amarin da ya raba mutane da dama da mahallansu.
Kazalika wasu rahotanni a yau Juma'a sun tabbatar da cewa Hukumar agajin gaggawa ta SEMA ta iso garin Nguru domin kididdige adadin wadanda bala'in ambaliyar ruwan ya shafa.
Ishaq Rabi'u Ishaq daya ne daga cikin mazauna Nguru ya ce abin da dan majalisar ya aikata aiki ne irin na Sayyadina Umar a lokacin yana Khalifan Muslumci.
Idan ba a manta ba, ko a 'yan satikan da sukan da suka wuce an gano dan majalisar a cikin magudanan ruwa yana yashe su tare da jama'arsa, kafin daga bisani a gano shi a makabarta yana feshin ciyawa tare da gyara wasu kaburburan da suka rufta.







No comments:
Post a Comment