Mai neman takarar Kansilan Unguwar Bulabulin a karamar hukumar Nguru a karkashin jam'iyyar PDP Hon. Fatima Musa Walida ta kaddamar da neman takararta ta neman Kansilan Unguwar.
An kaddamar da neman takarar ce a Asabar din nan a Cibiyar kallo ta Bulabulin( Bulabulin View center) cikin wani gagarumin biki da daruwan 'yan jam'iyyar suka halarta.
An gabatar da jawabai daban-daban a wurin taron da galibin mahalartansa suka tashi cikin murna.
A jawabinsa na maraba, Shugaban jam'iyyar PDP na Bulabulin Rabi'u Maikaratu ya gode wa mahalarta taron tare da yin fatan a watse taro lafiya.
Rabi'u Maikaratu ya kuma ce jam'iyyar PDP na marhabin da duk wani danta da ya nuna sha'awar tsayawa takara, domin a matsayin su na iyayen jam'iyya dole ne su bi da kowa daidai.
Rabi'u Maikaratu ya ce izuwa yanzu jam'iyyar PDP ba tsayar da dan takarar Kansila ba, to amma sai dai kowanne dan jam'iyya na hakki ya nema sannan kuma ya kaddamar da nemansa kamar yadda Walida ta kaddamar.
A nasa bangaren uban taron wanda kuma shi ne dan takarar shugancin karamar hukumar a karkashin jam'iyyar PDP Hon. Sani Garba Sharu ko Sani Gida-Gida ya yaba da yadda aka gudanar da taron.
Ita kuwa a nata jawabin da ta yi wa 'ya'yan jam'iyyar, mai neman takarar Kansilan ta Bulabulin Hon. Fatima Musa Walida gode wa Allah (SWT) ta yi tare da nuna jin dadinta game da yadda aka gudanar da taron.
Hon. Walida a jawabin ta kuma bayyana kudurorinta, wadanda ta ce idan aka zabe ta Kansila zata aiwatar wa mutanen unguwar.
Kudurorin nata dai sun hada da:
1. Kirkiro wasu hanyoyin hikima na dadada wa marayun da suke shan wahala a unguwar tare da tallafa musu da littafai da kayan makaranta domin su ma su sami rayuwa nagartacciya.
2. Za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin a ciccike ramukan da suke unguwar ta yadda za a hana ruwa kwanciya nan gaba.
3. Za ta gyara Famfunan da suka lalace wadanda aka yi watsi da su sannan kuma ta yi kokarin gina karin wasu sabbi a fadin unguwar.
4. Akwai kuma wani shiri na musanman da zata kirkiro na ciyar da unguwar gaba.
Hon. Walida daga karshe ta gode wa mahalarta taron tare da yin addu'o'in samun nasara a zaben kananan hukumomi da na kansiloli mai zuwa.







No comments:
Post a Comment