Daya daga cikin masu son jam'iyyar PDP ta ba su tikitin takarar Kansila a Nguru Hon. Fatima Musa Walida, ta ce ko a jikinta zargin rashin cancanta neman takara da wata mambar jam'iyyar ta yi musu.
Hon. Walida ta kuma yi alkawarin sai ta ba wa marada kunya idan ta zama Kansila a zaben kananan hukumomi da na kansilolin jiha mai zuwa.
Tana mai tabbatar da cewa a neman takarar ta babu gudu babu ja da baya.
Walida wacce ke naman takarar Kansilar unguwar Bulabulin ta bayyana hakan ne a yammacin ranar Litinin a yayin da take mayar da martani kan zargin rashin cancantar tsaya wa takara da wata mambar jam'iyyar ta yi musu a ranar Lahadi.
Hon. Walida ta fada wa wannan Dandali cewa ita ko a jikinta don an sami wata a ra'ayinta ta ce ba su cancanci takara ba domin tana da damar ta fadi hakan.
Ta ce Tsarin mulkin kasa ya ba ta dama kuma mutanen da suke burin tozarta wasu to shirya su ne za su tozarta.
Ta ci gaba da cewa kalaman matar ba za su sanyayar mata da gwuiwa ba, hasali ma kwarin guiwa suka ba ta domi dama a wajen Allah take nema.
Daga nan sai ta jaddada wa magoya bayanta cewa alkawaran da ta dauka idan ta zama Kansila za ta cika su ta yadda har 'yan adawa ma za su sha mamaki.
Hon. Walida ta yi wani abu mai kama da jirwaye mai kamar wanka ga 'yan adawa, ind ta ce ai idan ana Sallah to fa ba a magana, zai yi wuya dan Adam yayi komai daidai.
Walida wacce ke magana cikin raha da wannan Dandali ta wayar salula ta ce, ta yi amannar cewa dan Adam tara yake bai cika goma ba, wanda hakan ke nuna cewa babu wani dan Adam zai ce dari bisa dari yana aikata daidai ko da kuwa kuskuren nasa bai fito fili ba.
Ta ce tabbata ko ita ma matar da yi wannan kwatance ba ta isa ta ce tana aikata komai daidai ba, ballantana kuma har ta yi tunanin ta fi kowa.
Ta kara da cewa a baya an sha ba su labarin cewa an sami mutanen kirkin da Allah ya jarabe su da watsewa, wasunsu kuma mutanen banza ne sai Allah ya jarabce su da shiryuwa.
Ta ce mutum dai ya iya bakinsa ba dan waninsa ba ko dan kansa da iyalansa, domin rayuwar yau ba tabbas ne da ita ba.

No comments:
Post a Comment