Wednesday, May 29, 2019

Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni ya ayyana dokar ta-baci a fannin Ilmi a jihar

Gwamna Buni na jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni ya sanar da sanya dokar ta-baci a fannin Ilmin Firamare da na Sakandare a fadin jihar.

Jaridar Daily Truth ta rawaito cewa gwamna Buni wanda aka rantsar a yau Laraba ya fadi hakan ne a jawabinsa na rantsuwar kama aiki da aka gudanar a dakin taro na Banquet a gidan gwamnati a garin Damaturu.

Mai Mala Buni ya ce matakin ya dauke shi ne domin bunkasa ginshikin da tsohon gwamna Ibrahim Gaidam ya assasa a sashen.

Jaridar ta ce gwamna Buni ya kuma yi alkawarin samar da cibiyar kula da lafiya daya a kowace unguwa cikin unguwanni 178 na jihar, tare da samar da Tiraktoci ga manoma a kananan hukumomin jihar 17 a farkon damuma.

Ta bangaren ababen more rayuwa kuma, jaridar ta rawaito cewa, gwamna Mai Mala Buni ya yi alkawarin kammala aikin hanyoyin da ya gada daga tsohuwar gwamnati, tare da gina karin wasu sabbi da suka kunshi hanyar Gujba— Ngalda, da Tikau—Jajere, da Dogon Kuka—Jajere da kuma hanyar Yusufari—Machina da dai sauransu.

Kazalika Mai Mala Buni ya fada cewa zai gina kasuwanni na zamani( Modern Markets) a manyan garuruwan jihar da suka hada da Potiskum da Damaturu da Gashu'a da Nguru da Gaidam da Buni-Yadi da kuma Ngalda, tare da gina tashar Tireloli a Potiskum da wasu garuruwa.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za kuma ta farfado da masana'antun jihar da suka durkushe na tsawon shekaru domin bunkasar kudaden shiga na jihar.

No comments:

Post a Comment